Oshiomhole: Rikicin cikin gida ya kawowa APC tasgaro a jihar Ribas

Oshiomhole: Rikicin cikin gida ya kawowa APC tasgaro a jihar Ribas

Jam’iyyar APC ta bayyana abin da ya sa jihar Ribas ta kufce mata a zaben da ya gabata. Shugaban jam’iyyar na kasa, Kwamred Adams Oshiomhole ne ya fito ya bayyana wannan a Ranar Litinin.

Adams Oshiomhole yake cewa gaza magance sabanin da aka samu a cikin gidan APC ya sa jam’iyyar ta rasa jihar Ribas. An samu rikicin cikin gida ne a APC a dalilin wasu rashin jituwa.

Oshiomhole ya yi wannan bayan ne a Ranar 9 ga Watan Satumba, 2019, wajen kaddamar da shugabannin rikon kwarya na jam’iyyar a jhar ta Ribas. A nan ne ya koka da abin da ya faru.

Baraka ta barke ne tsakanin Magoya bayan tsohon gwamna kuma Minista Rotimi Amaechi da wadanda ke tare da Sanata Magnus Abe a cikin jam’iyyar APC. Wannan ya kawowa APC cikas.

Kwamared Oshiomhole yake cewa: “Duk ku na sane cewa kusan shekara guda kenan da kotun koli ta rushe zaben shugabannin da APC ta yi a Mazabu da kananan hukumomi da kuma jiha.”

KU KARANTA: Buhari da Atiku za su san makomarsu game da zaben 2019

“Wannan ya jawo APC ta rasa ginin jam’iyya a jihar Ribas duk da mun san cewa mu na dinbin Mabiya a jihar. Wannan ya sa yanzu majalisar NWC ta fara shirin sake kafa APC a jihar Ribas.”

Shugaban na APC ya nuna takaicin yadda sabanin Jiga-jigan jam’yyar ya jawo su ka tashi a tutar babu a zaben bana. Oshiomhole ya ce kusoshin jam’iyyar sun ki yin sulhu har APC ta shiga rudu.

A cewarsa, sun yi da-na-sanin yadda manyan ‘Ya ‘yan jam’iyyar su ka haddasa abin da ya je ya kai, ya komo APC ta samu kan ta a cikin matsala. Yanzu jam’iyyar ta kama hanyar gyara don gaba.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel