Majalisar wakilai ta aika sammaci ga wasu manyan hadiman gwamnatin Buhari guda uku

Majalisar wakilai ta aika sammaci ga wasu manyan hadiman gwamnatin Buhari guda uku

Kwamitin wucin gadi da majalisar wakilai ta kafa domin kula duba aiyukan hukumar cigaban yankin kudu maso kudu (NDDC) ya aika sammaci ga gwamnan babban bankin kasa (CBN), Godwin Emefiele, bisa yin watsi wasu muhimman aiyuka.

Kazalika, kwamitin majalisar ya aika wani sammacin ga mukaddashin babban darektan NNDC da kuma wasu manyan jami'ai a hukumar.

A wani korafi da gwamnatin jihar Akwa Ibom ta gabatar a gaban kwamitin majalisar ta hannun kwamishinan kasa na jihar, gwamnatin Akwa Ibom ta ce NDDC ta yi watsi da aiyuka 384 da ta fara a jihar.

Shugaban kwamitin, Ossai Nicholas Ossai, ya ce ba a bawa hukumar NDDC hadin kan da ya kamata yayin da take gudanar da aiyuka a jihohin yankin kudu maso kudu.

Kazalika, kwamitin ya nuna damuwarsa a kan rashin bayyanar wani wakili daga CBN yayin zaman bin kwakwafi a kan binciken da take gudanar wa a kan aiyukan hukumar NDDC da aka yi watsi da su, lamarin da yasa kwamitin ya aika sammaci ga Emefiele.

Kwamitin ya bawa dukkan jami'an gwamnatin da ya gayyata wa'adin sati daya domin su bayyana a gabansa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel