Yanzu Yanzu: Atiku da Buhari za su san makomarsu a ranar Laraba yayinda kotun zabe ke shirin yanke hukunci

Yanzu Yanzu: Atiku da Buhari za su san makomarsu a ranar Laraba yayinda kotun zabe ke shirin yanke hukunci

Kotun zaben Shugaban kasa ta sanya ranar Laraba, 11 ga watan Satumba, a matsayin ranar da za ta yake hukunci akan karar da dan takrar jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a zabe da ya gabatar, Alhaji Atiku Abubakar ya shigar, akan nasarar zaben Shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Kwamitin mutum biyar karkashin jagorancin Justis Mohammed Garda sun jingine hukuncin karar, a ranar 21 ga watan Agusta, inda suka bayyana cewa za a sanar da bangarorin da abun ya shafa bada jimawa ba bayan lauyoyin da ke shari’an sun rubuta jawabansu na karshe.

Bayanai da muka samu daga majiyarmu ta Thisday ta bayyana cewa kotun zaben ta sanya gobe Laraba, domin yanke hukunci, kwanaki biyar kafin karewar wa’adin karar.

Daya daga cikin lauyoyin gwamnati akan lamarin, wanda ya nemi a boye sunansa, yya tabbatar da cewar kotun zabe ta sanar da ranar yanke hukunci ga bangarorin da abun ya shafa a ranar Talata, 10 ga wata Satumba.

Idan haka yanke hukuncin a gobe Laraba, zai zama ya fada cikin kwanaki 180 da doka ta tanadar domin kammala shari’an da ya shafi zabe.

KU KARANTA KUMA: Da dumi-dumi: Jama’a sun tsere daga gidajensu yayinda yan bindiga suka fatattaki mutane a kauyen Niger

Yayinda aka gudanar da zabe a ranar 23 ga watan Fabrairu, hukumar zabe mai zaman kanta a ranar 27 ga watan Fabrairu ta kaddamar da Shugaban kasa Muhammadu Buhari a matsayin wanda ya lashe zaben Shugaban kasar.

Sai dai Atiku da jam’iyyarsa sun nuna rashin amincewa inda suka tunkari kotu domin kalubalantar lamarin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel