Da dumi-dumi: Jama’a sun tsere daga gidajensu yayinda yan bindiga suka fatattaki mutane a kauyen Niger

Da dumi-dumi: Jama’a sun tsere daga gidajensu yayinda yan bindiga suka fatattaki mutane a kauyen Niger

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Niger tace wasu yan bindiga kimanin su 200 sun kai farmaki kauyen Kokori da ke karamar hukumar Shiroro a jihar, inda suka fatattaki mutane daga gidajensu.

Darakta Janar na hukumar, Mista Ahmed Inga ya fada ma Channels Television a wayar tarho cewa ya samu wani rahoto daga yankin, wanda ke nuna ga cewa yan bindiga sun kai mamaya da tsakar ranar Litinin, suna harbi ba kakkautawa a sama.

Yace ta kai har sun yi wa wasu mutane dukan tsiya har sai da suka fita daga hayyacinsu.

Shugaban hukumar agajin yace yan bindigan sun kai mamaya dukkanin gidajen kauyen, inda suke zubarwa da mutane da kayayyakin su ciki harda abinci, tufafin sawa, wayoyi, yayinda suka kuma yi masu fashin dabbobinsu.

Mista Inga wanda yace ba a kawo rahoton rasa rai ba tukuna, ya bayyana cewa mazauna kauyen sama da 300 sun tsere daga gidajensu ta daji da kuma ketare ruwa.

KU KARANTA KUMA: Daukar ma’aikata 10,000: Ku yi watsi da jerin sunayen da NPF ta fitar – Hukumar yan sanda ga masu neman aiki

Yace mafi akasarin wadanda abun ya shafa sun kasance mata da kananan yara.

A cewar Mista Inga, a yanzu haka wasu daga cikinsu na hijira a wata makaranta a Kagara da ke karamar hukumar Rafi a jihar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel