Yan Shi'an El-Zakzaky kadai muke hanawa zanga-zanga - IGP Adamu

Yan Shi'an El-Zakzaky kadai muke hanawa zanga-zanga - IGP Adamu

Hedkwatar hukumar yan sandan Najeriya ta saki jawabin cewa yan kungiyar Shi'ar Sheikh Ibrahim El-Zakzaky ta IMN kadai suka hana gudanar da muzahara ba sauran kungiyoyin Shi'a ba.

Sifeto Janar na hukumar ya bayyana hakan ne ta baki mai magana da yawun hukumar, Frank Mba, a jawabin da ya saki da ranar Talata, 10 ga watan Satumba 2019.

Jawabin yace: "Sakamakon tulin tambayoyi da ake mana kan haramtawa yan kungiyar Shi'ar El-Zakzky gudanar da muzahara, ya zama wajibi mu bayyanawa jama'a cewa yan kungiyar IMN kadai muka hana gudanar da muzahara."

"Saboda haka, sauran Musulmai masu murnar ranan Ashura a fadin tarayya na da damar gudanar da muzahararsu."

"Amma su yi hakan bisa ga dokoki kuma kada su bari wasu yan tada zauna taye su shiga cikinsu domin kawo hargitisi da tayar da tarzoma."

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel