Kaico: An gano gawar Farfesan OSUSTECH da masu garkuwa da mutane suka sace a Edo

Kaico: An gano gawar Farfesan OSUSTECH da masu garkuwa da mutane suka sace a Edo

- 'Yan sanda sun gano gawar Farfesa Gideon Okedayo na OSUSTECH da 'yan bindiga suka sace a ranar Alhamis

- An gano gawar farfesan ne a cikin wani daji a ranar Litinin inda 'yan sanda suka tabbatar cewa wadanda suka sace shi ne suka kashe shi

- An sace farfesan ne a garin Aloko Edo na jihar Edo yayin da ya ke hanyar zuwa kauyensu domin ziyara

An tsinci gawar Farfesa Gideon Okedayo na Jami'ar Kimiyya da Fasha ta Jihar Ondo (OSUSTECH) da wasu 'yan bindiga da ake kyautata zaton masu garkuwa da mutane ne suka sace kamar yadda Sahara Reporters ta tabbatar.

An sace Okedayo ne a Igara Road da ke garin Aloko Edo na jihar Edo yayin da ya ke hanyar zuwa kauyensu a ranar Alhamis.

Wata majiya daga jami'ar ta shaidawa Sahara Reporters a ranar Talata cewa an gano gawar malamin ne a cikin daji.

DUBA WANNAN: Sabbin ministoci 5 da ke da 'jan aiki' a gabansu

"Abin bakin ciki ne. Sun kashe Farfesa Okedayo. A daren jiya (Litinin) muka samu labarin mummunar kisar gillar da aka yi masa.

"'Yan sanda sun kira mu daga caji ofis inda suka ce an gano gawarsa.

"Sun tabbatar mana da cewa wadanda suka sace shi ne suka kashe shi. Wannan lokaci ne na bakin ciki ga dukkan mu a wannan jami'ar," kamar yadda ya fadi a hirar wayar tarho.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Mailfire view pixel