Bauchi: An baro alhazai biyu a kasar Saudiya bayan jirgi ya kammala jigilar maniyattan jihar

Bauchi: An baro alhazai biyu a kasar Saudiya bayan jirgi ya kammala jigilar maniyattan jihar

Mukashin Sakataren Hukumar Kula da Walwalar Maniyyatan Jihar Bauchi, Alhaji Kasim Danladi Shall ya bayyana cewa an baro maniyyatan jihar biyu a kasar Saudiyya saboda rashin lafiya da suke fama da shi.

Ya bayyana hakan ne a Filin Tashin Jirage na Abubakar Tafawa Balewa da ke Bauchi bayan ya isowar jirgin karshe da ya kwaso maniyattan jihar na bana da suka dawo gida.

Daily Trust ta ruwaito cewa jirgin da ke jigilar maniyyatan jihar, Max Air ya sauka a filin jirgen na Bauchi misalin karfe 4 na asuba dauke da fasinjoji 281.

Shall ya yi bayanin cewa maniyattan da ke rashin lafiyan suna jinya a wani asibitin kasar Saudiyya kuma za a dawo da su gida Najeriya da zarar sun samu sauki.

Mukadashin sakataren ya kuma bayyana cewa maniyattan jihar Bauchi hudu sun rasu yayin aikin hajjin na bana.

Ya yabawa Gwamna Bala Abdulkadir Mohammed saboda goyon baya da kulawa da ya dinga bawa hukumar kula da jin dadin alhazan yayin aikin hajjin na bana.

A jawabinsa, Shugaban kwamitin tsaro na alhazan, Sanata Adamu Ibrahim ya yabawa maniyattan saboda halayen kirki da suka bayyana yayin zaman su a kasa mai tsarkin kuma ya bukaci su cigaba da hakan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel