YANZU-YANZU: Rikici ya barke tsakanin yan sanda da yan Shi'a a Kaduna, an harbe 3 (Hotuna)

YANZU-YANZU: Rikici ya barke tsakanin yan sanda da yan Shi'a a Kaduna, an harbe 3 (Hotuna)

Labarin da ke shigo mana yanzu na nuna cewa yan kungiyar Shi'a ta IMN sun cika alkawarinsu a yau Talata na gudanar da muzaharar ranar Ashura duk da gargadin hukumar yan sandan Najeriya.

Yan kungiyar sun taru a kasuwar Wuse dake birnin tarayya Abuja misalin karfe 7 na safe kuma suka nufi shataletaken Berger.

Yan Shi'an sun watse a Abuja yayinda suka ga yan sanda sun nufo wajensu. Wannan abu ya kawo cinkoso a titunan gari.

A yanzu haka, an rufe manyan titunan Kubwa da Mararaba.

Hakazalia rahotanni daga jihar Kaduna na nuna cewa rikici yan barke tsakanin yan Shi'an da yan sanda a garin Kaduna inda kawo yanzu an bindige mutane uku. Sahara Reporters ta ruwaito.

Wasu da dama sun jikkata.

Wani mazaunin Kaduna, Abdu na Abdu ya bayyana mana cewa da sassafe sun ji harbe-harbe a babban titin Nnamdi Azikwe na jihar Kaduna.

Kalli hotuna:

YANZU-YANZU: Rikici ya barke tsakanin yan sanda da yan Shi'a a Kaduna, an harbe 3 (Hotuna)
Daya daga cikin wadanda aka harbe
Asali: Facebook

YANZU-YANZU: Rikici ya barke tsakanin yan sanda da yan Shi'a a Kaduna, an harbe 3 (Hotuna)
An kwashe wnai

Asali: Legit.ng

Online view pixel