Kungiyar Shi’a tace sai tayi gangamin Ashura, ta aika wasiku zuwa ga hukumomin waje

Kungiyar Shi’a tace sai tayi gangamin Ashura, ta aika wasiku zuwa ga hukumomin waje

Kungiyar Islamic Movement in Nigeria (IMN) ta gayyaci hukumomin kasar waje da kungiyoyin jama’a domin su lura da tsari tattakinsu na Ashura 2019 a Abuja a yau Talata, 10 ga watan Satumba.

Wasu ma’aikatan gwamnati da ofishoshin da ke kewaye da sakatariyar tarayya na babban birnin tarayya sun nuna damuwa kan labarin tattakin musamma da gargadin da sufeto janar na yan sanda, Mohammed Adamu yayi.

Wani ma’aikaci a ma’aikatar shari’a, Ibrahim Oguche, wanda yace ana ta tattaunawa a tsakanin ma’aikatan ma’aikatar game da tattakin musamman da ya kasance yana a daya daga cikin hanyoyin da sanya ran za a yi amfani dashi wajen tattakin, sai dai yace yaa sanya ran ba za a samu kowani matsala.

Wata ma’aikaciyar gwamnati da ta nemi a sakaya sunanta, tace tattakin da suke shirin yi zai hana ta zuwa aikinta.

A halin da ake ciki, IMN ta aika wasiku zuwa ga shugaban majalisar dinkin duniya, jakadun tarayyar turai da kuma ECOWAS a Abuja da kuma kungiyar kare hakkin dan adam inda suke sanar masu da shirin da rundunar yan sandan Najeriya keyi na kai hari a yayin tattakinsu na Ashura.

KU KARANTA KUMA: Tirkashi: Daga cewa na rufe idona zai bani kyauta, ban yi aune ba sai jin wuka nayi a makogwaro na - Matar da mijinta yayi yunkurin yankata

Kakakin kungiyar IMN, Abdullahi Musa yayi al’ajabin dalilin karfafa tsaro da aka yi akan juyayin Ashura wanda yace wadanda ba Musulmai ba ma suna yi tsawon shekaru 40 da suka gabata ba tare da matsala ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel