Kamfanin jiragen sama na British Airways ya soke tashin daruruwan jiragen sama

Kamfanin jiragen sama na British Airways ya soke tashin daruruwan jiragen sama

- Kamfanin jiragen sama na British Airways ya soke tashin daruruwan jiragen sama

- Hakan ya biyo bayan yajin aikin sa'o'i 48 da matukan jirgin kamfanin suka tafi

- Yajin aikin zai iya jawowa kamfanin asarar Pam miliyan 40 wanda daidai yake da dala miliyan 49

Daruruwan jiragen sama ne aka soke tashin su a ranar Litinin sakamakon yajin aikin sa'o'i 48 da matuka jirgin British Airways suka fara.

Kamfanin jirgin saman ya yi ittifakin cewa yajin aikin na kwanaki biyu zai shafi matafiya 195,000.

Yajin aikin ne ya kawo dalilin soke kaiwa da kawowar jiragen sama na kamfanin wanda hakan zai jawo a mayar wa matafiya kudi ko kuma canza musu lokacin tafiya.

Yajin aikin na matukan jirgin na daya daga cikin gagarumin yajin aiki a tarihin kamfanonin jiragen sama kuma na farko da matuka jirgin kamfanin su ka yi.

Kamfanin ya ce, "Bamu da masaniyar wadanne matukan jirgin ne ba za su fito aiki ba ko kuma wadanne jiragen ne ba zasu tashi ba. A don haka ne muka yanke shawarar soke duk kaiwa da kawowar jiragen saman."

Kamar yadda kungiyar matuka jirgin kamfanin British Airways din ta fada, yajin aikin kwana daya kacal zai ja wa kamfanin asarar kusan pam miliyan 40 wanda daidai yake da dala miliyan 49.

A watan Yuli ne matuka jirgin suka ki amincewa da karin albashi na 11.5% a cikin shekaru uku.

Shugaban kamfanin, Alex Cruz ya hori kungiyar da su cigaba da tattaunawa don kawo karshen yajin aiki.

A ranar Litinin ne kamfanin ya je shafinsa na yanar gizo ya rubuta: "Mun fahimci bacin rai da tsaikon da yajin aikin matuka jirgin yasa wa matafiyanmu. Bayan kokarin watanni da muka yi na ganin mun shawo kan matsalar, muna masu matukar bada akan abinda ke faruwa."

Kamfanin British Airways ya ce yana kai da kawowar mutane sama da miliyan 49 a duk shekara.

Akwai kuma yuwuwar samun tsaiko ko soke kaiwa da kawowar jiragen a ranar Laraba tunda zai iya yuwuwa matuka jirgin na wani waje.

"Yakamata kamfanin British Airways ya farka," inji Brian Strutton, sakataren kungiyar matuka jirgin kamfanin.

Akwai shirin wani yajin aikin nan da ranar 27 ga watan Satumba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel