'Yan fansho sun ce a shirye suke su mutu a gidan gwamnatin Benue

'Yan fansho sun ce a shirye suke su mutu a gidan gwamnatin Benue

'Yan fansho a jihar Benue karkashin kungiyar 'Concerned Pensioners' sun sha alwashin cigaba da zanga-zangar da suke yi a gidan gwamnati da ke Makurdi har sai gwamnatin jihar ta biya musu bukatunsu.

'Yan fanshon suna zanga-zanga ne kan rashin biyan su hakokinsu na tsawon watanni 20 inda suka mamaye tituna a jihar daga bisani suka shiga harabar gidan gwamnatin kamar yadda The Punch ta ruwaito.

Shugaban kungiyar, Peter Ikyado ya ce sun dauki matakin fara yin zanga-zangan ne saboda gwamnatin jihar ba ta dauki wani mataki ba kan wasikun da suka rubuta na neman a biya su hakokinsu.

Ya ce Gwamna Samuel Ortom na jihar ya yi alkawarin biyan su kudin fanshon watannin Afrilu da Mayun shekarar 2018 ne amma Ikyado ya ce '"muna bukatar da biya mu a kalla kudin watanni shida kafin mu janye zanga-zangar.

DUBA WANNAN: Sabbin ministoci 5 da ke da 'jan aiki' a gabansu

"Ba mu iya biyan kudin makarantan yaran mu kuma ba mu iya sayan abinci mai kyau da za mu ci. Kwanaki uku da suka gabata, mambobin mu uku sun mutu -David Atsanan, (Ushongo) Joel Ijir da Kiishi Dom (Gboko) yayin da wani Yaaakur ya samu karaya.

"Muna mutuwa. Iyayen ku na mutuwa amma ba ku damu da mu ba. Muna son mu mutu a nan gidan gwamnati. Yanzu mun zama 'yan fansho masu gudun hijira."

Kakakin Majalisar Jihar, Titus Uba da ya gana da masu zanga-zangar a gidan gwamnati ya roki su dakatar da zanga-zangan inda ya ce za a biya su albashin watanni biyu. Ya ce majalisar tana iya kokarin ta don ganin an biya su sauran kudadensu.

Uba ya ce majalisar ta amince da kudirin fansho na Benue wadda zai bayar da damar kafa Hukumar Fansho na Jihar Benue.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Mailfire view pixel