Sowore: Anyi musayar yawu tsakanin lauya da mai shari'a

Sowore: Anyi musayar yawu tsakanin lauya da mai shari'a

- A ranar Litinin ne mai shari'a Maha ta kotun tarayya suka yi musayar maganganu da wani lauya

- Abubakar Marshal dai lauya ne mai kare shugaban zanga-zangar #Revolutionnow, Omoyele Sowore

- Mai shari'ar ta zargi Abubakar da daukar hankalinta yayin zaman kotu

A ranar Litinin ne mai shari'a Nkeonye Maha ta kotun tarayya da je Abuja ta zargi lauya da daukar hankalinta yayin zaman Kotu.

Abubakar Marshal, daya daga cikin lauyoyi masu kare shugaban zanga-zangar #Revolutionnow#, Omoyele Sowore, ya tunkari mai shari'a a kotun kafin a fara zaman kotun.

Gwamnatin tarayya ce ke tsare da Sowore sakamakon zarginsa da take da yiwa gwamnatin zagon kasa bayan da ya hada zanga-zanga mai taken #Revolutionnow#.

KU KARANTA: Kotu ta kwace kujerar Sanata Manager, ta bayar da umurnin sake sabon zabe

A ranar Litinin ne Abubakar ya tabbatar cewa ba a maidawa mai shari'a Taiwo Taiwo shari'ar sati daya bayan Maha bata samu damar zaman kotun ba.

A musayar maganganu da aka yi tsakanin lauyan da mai shari'a, mai shari'a Maha ta zargi Abubakar da daukar mata hankali yayin zaman kotun.

A take lauyan yace, gara dai ya tunkari mai shari'ar a gaban kotun maimakon ya sameta da maganar a wani wajen da zai iya kawo zargi.

Ya bukaci a mika takardun shari'ar ga mai shari'a Taiwo Taiwo wanda ya dawo hutu.

Mai shari'ar ta ce wannan maganar ta hukuma ce kuma za a shawo kanta.

"Ya mai shari'a, akwai bukatar a mika takardun shari'ar ga abokin aikinki mai shari'a Taiwo Taiwo," cewar lauyan.

A maida martanin mai shari'ad, "Eh, akan hakan ne ka dami kotun, ka ke daukar hankalin mutane a gabana akan matsalar hukumar?"

Abubakar sai ya kara da cewa, "Toh mai shari'a, an sanar da ni ne takardun shari'ar suna tare da ke ne, abinda ya hana kotun mai shari'a Taiwo Taiwo dubawa tare da sagalar da sauran shari'ar gabanta."

Mai shari'ar sai tace: "Na fada, wannan maganar hukuma ce, ba kuma dalili bane da zaka zo kana damun kotuna."

Lauyan sai yace, "Na sani mai shari'a. Bana son zuwa kai korafi daga ni sai ke ne, shiyasa nazo gaban kotu."

A take mai shari'ar ta juya tare da fadin, "Kada ka kara zuwa kana damun kotuna akan hakan."

A yayin da mai shari'a Maha ke ganawa da manema labarai, tace "Ina rokon da ku san abinda zaku bada rahoto. Bani da hannu akan maganar."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel