Gwamnan jihar Borno ya kammala ayyuka 120 cikin kwanaki 100 a mulki

Gwamnan jihar Borno ya kammala ayyuka 120 cikin kwanaki 100 a mulki

Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya kammala ayyuka 120 cikin kwanaki 100 da yayi kan karagar mulkin jihar.

Wannan ya bayyana a jawabin da sakataren gwamnan jihar Borno, Usman Jidda Shuwa, ya saki inda ya bayyana kashe-kashen ayyukan da inda gwamnatin jihar ta gudanar da su.

Ya kara da cewa ba'a samu gudanar da ayyuka da yawa a Arewacin Borno ba saboda rikicin Boko Haram da yayi tsamari a yankin.

Yace: "Daga cikin ayyukan 120, anyi 61 a tsakiyar Borno, 43 a kudancin Borno sannan 9 a arewacin Borno saboda ayyukan sojoji dake gudana a wajen."

"A rabe-raben ayyukan 61 da akayi a cikin tsakiyar Borno, an yi 20 a Konduga, musamman samar da ruwan sha."

"An yi 14 a tsakiyar Maiduguri, 10 a Jere, 5 a Bama, 3 a Mafa, 3 a Dikwa, 3 a Ngala, sannan 3 Kala-Balge."

KU KARANTA: Da kyau: Kakakin majalisar wakilai, Gbajabiamila, ya nada diyar Ganduje matsayin babbar hadimarsa

A bangare guda, Bayan kwanaki 100 na farko a bisa kujerar mulki, wata cibiyar dimokuradiyya ta Afirka mai tushe a birnin Dakar na kasar Senegal, ta zabi gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, a matsayin gwamnan da ya fi kowanne kwazo a halin yanzu a Najeriya.

Cibiyar mai akidar dimokuradiyya ta ADAN, African Democracy Assessment Network, ta ayyana gwamna Ganduje a matsayin gwamnan da ya yi wa sauran gwamnonin Najeriya fintinkau ta fuskar kwazo a bisa kujerar mulki, lamarin da ta ce ya cancanci kyauta ta musamman.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel