Me yayi zafi: Nayi kokarin kashe kaina a lokacin dana bar ofis - Tsohon ministan Shari'a a lokacin Jonathan

Me yayi zafi: Nayi kokarin kashe kaina a lokacin dana bar ofis - Tsohon ministan Shari'a a lokacin Jonathan

- Tsohon ministan shari'a na Najeriya a lokacin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, ya bayyana wani sirri a rayuwar shi

- Tsohon ministan Mohammed Adoke ya bayyana cewa a lokacin da ya bar kan mulki sai da yayi yunkurin kashe kanshi daga baya ya fasa

- Ya ce yayi hakan ne saboda irin matsin lambar da yake samu daga wajen hukumar yaki da cin hanci da rashawa akan zargin satar kudi da yayi

Tsohon ministan Shari'a a lokacin tsohon shugaban kasa Goodluck Ebele Jonathan, Mohammed Adoke, ya bayyana cewa yayi kokarin kashe kanshi a lokacin da kammala aiki ya bar ofis, saboda tsabar zargin da hukumar cin hanci da rashawa take yi masa na satar kudi.

Adoke dai yana daya daga cikin mutane da ake zargi a badakalar kudin mai na Malabu, sannan kuma ana zargin shi da hannu a biliyan shida na kudin tsohon shugaban kasa janar Sani Abacha da aka samo a tsibirin Jersey.

A wani littafi da ya rubutu mai suna 'Burden of Office' wanda zai sake shi kwanan nan, Adoke wanda ya shiga ofis a watan Afrilun shekarar 2010 ya kuma bar ofis a watan Mayun shekarar 2015, a lokacin da Jonathan ya bar kan mulki, ya ce bai ji dadin zargin da ake yi masa ba na cin hanci da rashawa.

KU KARANTA: Tashin hankali: Budurwa ta kone wani saurayi kurmus akan ya hanata naira 200 da take bin shi

Adoke mai shekaru 56, ya ce lokacin yana cikin gidan a kasar Netherland sai yayi tunanin kawai ya fado daga kan bene ya mutu kowa ma ya huta.

Ya bayyana cewa ya zabi ya cigaba da rayuwa ne saboda ya tsaya ya kare kanshi akan zargin da ake yi masa wanda ya san cewa bai aikata ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel