Tirkashi: Na daina zuwa coci ne bayan na gano addinin Kiristanci buge-bugen iska ne - Efia Odo

Tirkashi: Na daina zuwa coci ne bayan na gano addinin Kiristanci buge-bugen iska ne - Efia Odo

- Fitacciyar jarumar kasar Ghana, Efia Odo ta bayyana wani dalilinta da ya sanya ta daina zuwa coci ibada kwata-kwata

- Jarumar ta ce ita ta kasa gane inda addninin Kiristanci ya sanya gaba, shine yasa ta daina zuwa cocin

- Ta ce ta yadda cewa akwai Allah kuma ta yadda da Annabi Isa, amma kuma gaskiya addinin Kiristanci ta san cewa akwai rudani a cikin shi

Fitacciyar jarumar kasar Ghana, Efia Odo ta bayyana cewa ta daina zuwa coci ne kwata-kwata bayan ta kasa gane inda alkibilar addinin Kiristanci ta sanya gaba.

Jarumar wacce kuma take wani shiri a gidan talabijin na Kwase TV, ta bayyana cewa ta yadda kwarai da gaske akwai Allah sannan kuma ta yadda da Annabi Isa, amma kuma addinin Kiristanci yana da rudani masu yawan gaske a tattare dashi da suke da rikitarwa.

"Lokacin ina yarinyar karama ina zuwa coci a kowanne lokaci, ina bin mahaifiyata muje tare, amma lokacin dana girma sai na daina zuwa, saboda na kasa gane alkibilar wannan addinin namu," in ji ta.

KU KARANTA: Tirkashi: Daga cewa na rufe idona zai bani kyauta, ban yi aune ba sai jin wuka nayi a makogwaro na - Matar da mijinta yayi yunkurin yankata

Da aka tambayeta akan tsattsauran ra ayi, Efia Odo ta ce a cikin hirar ta su:

"Ni ba mace ba ce mai tsattsauran ra'ayi. Ina yin rayuwata ne yadda naga ta fi mini, ya rage naku ku yadda da abinda na fada ko karku yadda."

Jarumar dai ta kasar Ghana yanzu ne tauraruwar ta ke haskawa a masana'antar fina-finai ta kasar Ghana.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel