Tashin hankali: Kudan zuma sun kai wa wani dan majalisar APC hari har gida, kwanaki uku da samun nasarar shi a kotu

Tashin hankali: Kudan zuma sun kai wa wani dan majalisar APC hari har gida, kwanaki uku da samun nasarar shi a kotu

- Rahotanni sun bayyana cewa kudan zuma sun mamaye gidan Honarabul Halims Agoda dake jihar Delta

- Kudan zuman da aka kasa gano daga inda suke sun zubo kasa sun mutu a kofar gidan dan siyasar bayan sun kasa shiga gidan

- Wani mutumi mai amfani da shafin sada zumunta na Facebookk shine ya wallafa hakan, inda ya bayyana cewa ikon Allah ne kawai ya hana kudan zuman shiga gidan dan majalisar

Wani rahoto da muka samu kwanaki uku bayan dan siyasar ya samu nasarar lashe zaben zama dan majalisa mai wakiltar Ethiope dake Asaba cikin jihar Delta.

Agoda dai ya fito takara ne a jam'iyyar APC mai mulki a ranar 23 ga watan Fabrairu, inda shi kuma abokin hamayyar sa, Benson Rolands Igbakpa ya fito a babbar jam'iyyar adawa ta PDP, kuma aka nuna cewa shine yayi nasara, kafin daga baya kotu ta kwace kujerar.

Kotun ta bayyana Agoda a matsayin wanda ya lashe zaben, inda ta nemi kuma a bashi takardar zama dan majalisar yankin.

KU KARANTA: Abinda yasa shugaba Buhari baya daukar mataki akan masu zagin shi a shafukan sadarwa - Gwamnatin tarayya

Wani mai amfani da shafin sadarwa na Facebook mai suna Believe Egbe ya wallafa wani rubutu, inda yake cewa kudan zuma sun nemi shiga gidan dan majalisar kwanaki uku bayan an bayyana cewa ya samu nasara a kotu.

Egbe ya bayyana cewa kudan zuman sun mutu a kofar gidan dan majalisar, bayan sun nemi hanyar shiga sun rasa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel