Masu garkuwa da mutane sun sace matafiya 6 a hanyar Abuja zuwa Kaduna

Masu garkuwa da mutane sun sace matafiya 6 a hanyar Abuja zuwa Kaduna

Rundunar 'yan sandan Najeriya reshen jihar Kaduna ta tabbatar da sace matafiya shidda a kan babbar hanyar Kaduna zuwa Abuwa.

A jawabin da kakakin rundunar 'yan sandan jihar Kaduna, DSP Yakubu Sabo, ya fitar, rundunar ta ce lamarin ya faru ne ranar Lahadi da daddare yayin da matafiyan ke yin bulaguro a kan babbar hanyar da ta yi kaurin suna wajen sace mutane domin yin garkuwa da su.

Labarin garkuwa da mutanen na zuwa ne a cikin kasa da sa'o'i 24 bayan rundunar 'yan sandan jihar Kaduna ta sanar da kashe masu garkuwa da mutane uku tare da kama wasu 25 a kan babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna da kuma daga Kaduna zuwa Zaria.

DSP Sabo ya bayyana cewa wasu 'yan bindiga ne cikin kakin sojoji suka sace mutanen bayan sun tare wata motar fasinja da misalin karfe 11:40 na dare a daidai kauyen Rijana dake kan hanyar Abuja zuwa Kaduna.

DUBA WANNAN: Masu garkuwa da mutane sun kone gawar wani matashi saboda ba a biya su kudin fansa ba

Kakakin ya kara da cewa 'yan bindigar sun shiga jeji da fasinjojin da suka sace.

A cewarsa, rundunar 'yan sanda ta gaggauta aika jami'anta dake sintiri a kan babban titin zuwa wurin da abin ya faru kuma har sun yi musayar wuta da 'yan bindigar.

Sakamakon musayar wutar ne 'yan bindigar suka saki mutane 2 daga cikin mutanen 6 da suka kama, a cewar DSP Sabo.

Kazalika, ya bayar da tabbacin cewa rundunar 'yan sanda na cigaba da kokarin ganin ta kubutar da sauran fasinjoji hudu da 'yan bindigar ke rike da su har yanzu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel