Zaben 2019: Kotun zaben Kaduna ta tabbatarwa PDP nasara a zaben majalisa

Zaben 2019: Kotun zaben Kaduna ta tabbatarwa PDP nasara a zaben majalisa

Kotun sauraron korafe-korafen zaben majalisar dokokin tarayya da kumata jiha a Kaduna ranar Litinin ta tabbatar da nasara ga Mista Tanimu Musa.

Mista Samuel Hardware ne na jam’iyyar APC ya kalubalanci nasarar Tanimu na jam’iyyar PDP a kotun inda ya ki amincewa da nasarar da Tanimu ya samu a zaben ranar 9 ga watan Maris.

KU KARANTA:NYSC ta fatattaki dalibai 8 da su kayi karatu a kasar waje daga aikin bautar kasa

A lokacin wannan shari’a wadda aka dauki tsawon awa guda ana yenta, alkalin dake jagorantar shari’ar Jastis Adamu Sulaiman tare da abokan aikinsa ya kori karar.

Hukuncin da Jastis Daniel ya karanto ya na cewa, wanda ya shigar da karar ya gagara kawo wa kotu hujjoji gamsassu game da kalubalantar nasarar abokin karawarsa da ya keyi.

“A cikin korafin dole ya kasance akwai rokon bukata zuwa ga kotu daga bangaren mai karar wanda bai yi hakan ba.” A cewar Daniel.

Haka zalika, wanda ke karar bai fadi adadin kuri’un da yake ikirarin cewa anyi aringizonsu ba, kana kuma rumfunan da ya ce abin ya shafa ma bai ambacesu ba gaba daya.

Kotun ta kara da cewa, dukkanin wata shaida da ake bukata daga wurin Samuel bata samu ba a don haka wannan dalilin ne ya tilasta mata yin watsi da wannan karar.

Da yake magana a kan wannan hukuncin, Mista Tanimu wanda shi ne yayi nasara a shari’ar ya bayyana wannan abu a matsayin wata nasara wadda take daga wurin Ubangiji.

Ga abinda Tanimu ya fadi a kalamansa: “Wannan shari’a dai hukunci ne na Allah, Allah yayi ikonsa a cikinta, ina cike da farin ciki mai tarin yawa kuma yanzu ne nasan cewa gatan daidaikun mutane ita ce kotu.”

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit Nigeria

Tags:
Mailfire view pixel