Buhari ya kebance da shugaban Red Cross a fadar Villa

Buhari ya kebance da shugaban Red Cross a fadar Villa

Kamar yadda jaridar The Punch, a yanzu dinnan, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kebance tare da shugaban kungiyar bayar da agaji ta kasa-da-kasa wato Red Cross, inda suke ganawa da juna cikin fadar Villa da ke babban birnin kasar nan na Tarayya.

Shugaba Buhari na tsaka da ganawa da Mr Peter Maurer, shugaban kungiyar bayar da agajin gaggawa da jin kai wajen tseratar da rayuwa da kuma kare martabar wadanda munanan rikici suka addaba gami da sauran tashin-tashin masu barazana ga zaman lafiyar bil Adama.

Mr Maurer a yayin zantawa da manema labarai na fadar shugaban kasa, ya yi tsokaci musamman a kan makomar daya daga cikin daliban makarantar Dapchi wadda har yanzu take tsare a hannun 'yan kungiyar masu tayar da kayar baya ta Boko Haram, Leah Sharibu, da kuma ragowar 'yan matan Chibok.

Yayin zayyana dalilin ziyarar da ya kai wa shugaban kasa, Mr Maurer ya bayyana cewa manufa ce ta yi wa shugaban kasar karin haske kan al'amura da suka shafi jinkai da bayar da agajin gaggawa a Najeriya musamman a yankin Arewa maso Gabashin kasar.

Hakazalika jaridar mu ta Legit.ng ta ruwaito cewa, shugaban kasa Buhari a yau Talata, ya yi wata ganawar sirri da shugabannin hukumomin tsaron Najeriya a fadarsa ta Aso Rock dake birnin tarayya, Abuja.

KARANTA KUMA: An yi mummunar arangama tsakanin 'yan sanda da mabiya akidar shi'a a jihar Katsina

Ganawar ta kunshi babban sufeton 'yan sanda na kasa (IGP), Mohammed Adamu, mai bai wa shugaban kasa shawara a kan harkokin tsaro (NSA), Babagana Monguno, da shugaban hukumar tsaro ta sirri (NIA), Ahmed Rufa'i Abubakar.

Wata majiyar rahoto mai tushe a fadar shugaban kasa ta ce ganawar ba za ta rasa nasaba da matsalolin tsaron cikin gida da ake fama da su da kuma hare-haren kin jinin baki da aka kai wa 'yan Najeriya mazauna kasar Afrika ta Kudu a baya-bayan nan.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel