Ramaphosa ya yi Allah wadai kan hare-haren da ake yiwa baki a Afirka ta Kudu

Ramaphosa ya yi Allah wadai kan hare-haren da ake yiwa baki a Afirka ta Kudu

A yayin da ya ke tofa albarkacin bakin sa kamar yadda Muryar Duniya ta ruwaito, shugaban kasar Afirka ta Kudu, Cyril Ramaphosa, ya bayyana damuwa tare da yin Allah wadai da hare-haren kin jinin baki da suka auku a kasar a baya-bayan nan.

Cikin 'yan kwanaki kadan da suka gabata a baya-bayan nan, akalla mutane 10 sun rasa rayukansu a sanadiyyar munanan hare-haren da aka zartar kan baki da dukiyoyinsu mazauna Afrika ta Kudu, inda galibi suka kasance ‘yan Najeriya.

Wannan mummunan lamari ya sanya gwamnatin Tarayya ta ce a ranar Laraba za ta fara jigilar kwaso 'yan Najeriya mazauna kasar sakamakon hare-haren kiyayya da nuna kin jinin su da ya sake ta'azzara a kwana-kwanan nan.

Jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayar da umarnin a fara dawo da duk 'yan Najeriya da ke sha'awar dawowarsu gida nan take.

A sanarwar da jakadan Najeriya a kasar Afirka ta Kudu, Godwin Adamu, ya gabatar a jiya Litinin cikin birnin Johannesburg, ya ce a karo na farko kamfanin Air Peace zai fara jigilar kwaso 'yan Najeriya 320 a ranar Laraba.

KARANTA KUMA: Tsohon shugaban Najeriya Jonathan zai ziyarci kasar Mozambique

Shugaban kasar ya bayar da umarnin ne biyo bayan samun cikakken rahoto daga tawaga ta musamman da ya tura kasar Afirka ta Kudu bisa jagorancin Ambasada Ahmed Abubakar.

Shugaba Buhari ya jadada cewa akwai bukatar gwamnatin kasar Afirka ta Kudu ta dauki kwararran matakai domin kawo karshen hare-haren da ake kai wa baki da ke zaune a kasar.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Online view pixel