A tashi a farga a kan harkar ilimi a Najeriya - ASUU

A tashi a farga a kan harkar ilimi a Najeriya - ASUU

Kungiyar malaman jami'o'in Najeriya ASUU, ta kirayi gwamnatin tarayyar Najeriya da ta gaggauta kaddamar da dokar ta baci kan harkokin ilimi a kasar nan.

Kiran kungiyar na zuwa ne a ranar Litinin yayin da ta gudanar da taron manyan jiga-jiganta na kasa a jami'ar nazarin noma ta birnin Abeokuta da ke jihar Ogun kamar yadda jaridar The Cable ta ruwaito.

Cikin wata sanarwa da sa hannun shugaban kungiyar na kasa, Farfesa Biodun Ogunyemi, ya bayyana damuwa dangane da gazawar gwamnatin tarayya a kan kaddamar da dokar ta baci kan harkokin ilimi kamar yadda ministan ilimi, Adamu Adamu ya zayyana a shekarar 2017.

Ogunyemi ya ce tuni da an ribaci wannan lokacin wajen sadaukar da kai domin fuskantar kalubalai da su ka yiwa harkokin ilimi dabaibayi a kasar.

Har ila yau kungiyar na ci gaba da zargin gwamnatin Najeriya da jinkirin aiwatar da yarjejeniyar da suka kulla tun a shekarar 2009 game da yadda za a inganta yanayin aiki a jami'o'i, da kuma rashin biyan mambobinta kudaden alawus da wasu sauran bukatu da ta cancanta.

KARANTA KUMA: Ashura: An jibge 'yan sanda domin hana 'yan shi'a tattaki a jihar

Bababu shakka kungiyar ASUU ta dade tana kai ruwa rana da gwamnati a kan bukatunta ne neman a inganta makamar aiki da kuma jami'o'i, lamarin da sau da dama ke haifar da yajin aiki masu hangen nesa ke hanin yana matukar yiwa karatu a jami'o'in kasar nan zagon kasa.

Kazalika kungiyar ASUU ta kirayi gwamnatin Najeriya da ta tashi ta farga domin magance matsaloli na rashin tsaro, tattalin arziki da kuma yaye kangin talauci da ya lullube al'ummar kasar nan, lamarin da ta ce ya sanya wasu da dama neman arziki da kuma tsira a wasu kasashen.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Online view pixel