Yawan adadin yan Najeriya da ke son barin kasar Afrika ta Kudu ya tashi daga 400 zuwa 640

Yawan adadin yan Najeriya da ke son barin kasar Afrika ta Kudu ya tashi daga 400 zuwa 640

Abike Dabiri-Erewa, shugabar hukumar yan Najeriya mazauna waje, tace yan Najeriya 640 ne suka nuna ra’ayin son dawowa gida daga kasar Afrika ta Kudu.

Dabiri-Erewa ta bayyana hakan ne yayinda take amsa tambayoyi daga yan jarida a ranar Litinin, 9 ga watan Satumba.

Da farko Godwin Adama, karamin jakadan Najeriya a Afrika ta Kudu yace yan Najeriya 400 ne suka nuna ra’ayin dawowa gida.

Adama wanda ya bayyana haka ga Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) a ranar Lahadi, yace yan Najeriya na cigaba da nuna ra’ayin son dawowa.

Hare-haren da aka kaddamar a kasar a Afrika ta Kudu a kwanan nan ya shafi yan Najeriya da sauran yan kasashen Afrika.

Domin zanga-zanga kan haka, Najeriya ta kaurace ma taron kungiyar tattalin arziki na duniya wanda aka gudanar a kasar.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari har ila yau ya tura wakilai zuwa ga Gwamnatin Afrika ta Kudu akan lamarin.

Jirgin Air Peace ta amince zata dawo da yan Najeriya wadanda ke da ra’ayin dawowa gida kyauta.

KU KARANTA KUMA: Yan bindigan Katsina sun saki mata 3 da wasu mutane

A lokacin da ta bayyana a gaban kwamitin majalisar dattawa kan kasar waje a ranar Litinin, Dabiri-Erewa tace jirage guda biyu za su kwashi yan Najeriya wadanda ke da ra’ayin dawowa gida.

Tace Gwamnatin Tarayya har yanzu tana neman a biya wadanda hare hare ya shafa diyya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Mailfire view pixel