NYSC ta fatattaki dalibai 8 da su kayi karatu a kasar waje daga aikin bautar kasa

NYSC ta fatattaki dalibai 8 da su kayi karatu a kasar waje daga aikin bautar kasa

Shugaban hukumar NYSC na jihar Kano, Ladan Baba ya ce hukumarsu ta kori mutane 8 da suke ikirarin sunyi karatu a kasar waje daga aikin bautar kasa saboda rashin yin cikakkiyar rajista.

Baba ya fadi wannan maganar ne a ranar Litinin wurin bikin yaye rukunin B na masu bautar kasa na shekarar 2019 bayan sun kammala samun horo na musamman a sansanin hukumar na din-din-din dake Kusalla a karamar hukumar Karaye.

KU KARANTA:Buhari ya nadawa hukumar NDLEA sabon sakatare

Shugaban ya ce wasu daga cikin daliban an dakatar da su ne tun a lokacin da suke kokarin yin rajista a yanar gizo saboda sun gagara bada gamsasshiyar shaida game da takardunsu na digiri.

“Alal hakika da dama daga cikinsu ba su ko iya yin magana da ingantacce turanci. Abinda ya fi damunmu shi ne karya suke babu wani karatun da suka yi, kawai dai sun yi amfani ne da haramtacciyar hanya domin samun kwalayen digirin.

“Mun samu labarin cewa wasu daga cikinsu a nan Kano suka shirya wannan makarkashiyar ta su. Akwai bukatar gwamnati da sauran hukumomin tsaron Kano su kula sosai domin dakatar da irin wannan mugun aiki.” Inji Baba.

Baba ya kara da cewa, a cikin ‘yan bautar kasa 1,700 da aka tura Kano cikin rukunin B na wannan shekarar, mutum 1,592 ne suka halarcin horon makonni uku a sansanin na Kano.

Ya kuma yi kira ga masu bautar kasan da su jajirci wurin kawowa kasar Najeriya cigaba ta hanyar amfani da ilimi da kuma hazakarsu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel