Yan bindigan Katsina sun saki mata 3 da wasu mutane

Yan bindigan Katsina sun saki mata 3 da wasu mutane

Yan bindigan da suka addabi jihar Katsina sun saki akalla mutane biyar ciki harda mata uku wadanda yan fashin suka yi garkuwa da su, daga cikin yarjejeniya tsakanin gwamnatin jihar da yan bindigan.

Gwamna Aminu Bello Masari ne ya bayyana haka a yayinda yake hira da wasu tubabbun yan fashi a kauyen Baranda a karamar hukumar Batsari da ke jihar.

Masari yace an saki wadanda lamarin ya cika da su ne a ranar Lahadi sanan kuma cewa a halin yanzu an mayar da su ga iyalansu.

Ya cigaba da cewa yan fashin har ila yau sun sha alwashin sakin sauran mutanen da ke hannunsu.

Bisa hakan ne gwamnan yayi kira ga al’umman jihar da su daina kai hari akan tubabbun yan bindiga idan suka ziyarci wuraren bauta da kuma kasuwanni don gudanar da kasuwanci da kuma bauta.

KU KARANTA KUMA: Tsantseni: Yadda karamar hukumar Daura ta gyara 'burtsatse' 26 da N4.1m

A lamari mai kama da haka ne kwamishinan yan sanda, CP Sanusi Buba ya bada umurni ga yan bindiga da su mika makaman su, su kuma yi aiki sau da kafa don dawo da zaman lafiya a jihar.

Wassu daga cikin yan fashin, Abdullahi Ibrahim da Fulani Shafe sun sha alwashin mika makaman su don cigaba da samar da zaman lafiya a jihar kamar yanda suka yabi Gwamna Masari akan kirkiro shirin da yayi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel