Ba zamu iya dakatar da hare-haren da ake kai wa 'yan Najeriya ba - Gwamnatin Afrika ta Kudu

Ba zamu iya dakatar da hare-haren da ake kai wa 'yan Najeriya ba - Gwamnatin Afrika ta Kudu

Ministan tsaron kasar Afrika ta Kudu, Nosiviwe Mapisa-Nqakula, ta ce wasu batagarin 'yan ta'adda ne ke shirya hare-haren da ake kai wa bakin haure dake zaune a kasar tare da bayyana cewa gwamnati ba zata iya dakatar da hare-haren ba.

Uwargida Mapisa-Nqakula, wacce ta bayyana hakan yayin wata gana wa da kafar yada labarai ta eNCA dake kasar Afrika ta Kudu, ta bayyana 'yan kasar Afrika ta Kudu a matsayin fusattatu, tare da kafe wa a kan cewa gwamnatin kasar a zata iya hana rikicin dake faruwa ba.

"Maganar gaskiya ita ce mutanen mu sun fusata. Babu wata gwamnati da zata iya dakatar da abinda ke faruwa," a cewar ta.

Sai dai, ta bayyana cewa hare-haren basu da nasaba da siyasa.

"Mutane na cewa ana kai wa bakin haure ne hare-hare amma wannan ba shine karo na farko da muke fuskantar irin wannan matsala ba, mun fuskanci irin wannan matsaloli a baya. Wasu tsirarun 'yan ta'adda sun yi amfani da kalubalen da muke fuskanta wajen shirya hare-haren da ake kai wa bakin haure.

DUBA WANNAN: Tattakin mabiya Shi'a daidai yake da ta'addanci - IGP

"Akwai bakin haure da suka zo daga kasashen da ake fama da matsalar rashin aiki kuma sun zo basa bin doka da tsari kamar yadda ya dace, suna karya dokar kasar mu, wanda sakamakon haka ne yasa wasu 'yan ta'adda ke ganin suna da uzurin kai musu hari."

"Bai dace ba, ba ma jin dadin abinda yake faru wa. Akwai bukatar mu tattauna a kan wanna matsala. Mu na fama da fusatattun matasa kuma dole mu yi magana a kan hakan," a cewar ministar tsaron.

Uwargida Mapisa-Nqakula ta ce kasar Afrika ta Kudu na bukatar hadin kan gwamnatoci da masu ruwa da tsaki domin warware matsalolin da suke fuskanta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel