An yanke hukunci game da shari’ar Sanatocin Anambra Ekwunife da Ubah

An yanke hukunci game da shari’ar Sanatocin Anambra Ekwunife da Ubah

Kotu ta yanke hukunci game da karar da aka shigar ana kalubalantar nasarar da Sanata Ifeanyi Ubah da Sanata Uche Ekwunife su ka samu a zaben majalisar dattawa a zaben shekarar nan.

Kamar yadda labari ya zo mana a yau Litinin dinnan, 9 ga Watan Satumba, 2019, kotu ta ba Sanata Ifeanyi Ubah gaskiya a shari’ar da ake yi game da kujerar ‘dan majalisar Anambra ta Kudu.

Sanatan na jam’iyyar adawa ta YPP ya doke Cif Chris Uba na jam’iyyar PDP da kuma Andy Uba na jam’iyyar APC wanda su ke so kotu ta rushe nasarar da Ifeanyi Ubah ya samu a zaben 2019.

Andy Uba da Chris Uba duk ‘yan gida daya ne wanda su ka nemi kujerar majalisar dattawan kudancin jihar Anambra a bana. Jam’iyyar YPP ce ta bada mamaki inda Ifeanyi Uba ya yi nasara.

KU KARANTA: Kotu ta soke zaben tsohon gwamnan PDP da aka zaba Sanata a APC

Duk a jihar ta Anambra, Sanata Uche Ekwunife ce ta samu nasara a gaban kotun da ke sauraron korafin zaben na wannan shekarar. Uche Ekwunife ta yi galaba a kan Victor Umeh na APGA.

Sanata Victor Umeh ya shigar da kara ya na kalubalantar Uche Ekwunife ta PDP a kotu. Umeh ya gaza samun nasara wajen gamsar da kotu cewa shi ne ya lashe zaben Anambra ta tsakiya.

Alkali mai shari’a, Esther O. Haruna da sauran Alkalan da su ka duba korafin da aka shigar, sun yi fatali da karar Chris Uba da Victor Umeh. ‘Yan majalisun za su cigaba da wakiltar Mazabunsu.

Dazu kun ji cewa Ike Ekweremadu mai wakiltar mutanen Enugu ta yamma a majalisar dattawan Najeriya ya samu nasara a gaban kotun da ke sauraron korafi game da zaben na sa a Enugu.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Online view pixel