Yusuf Sambo - Hazikin matashin Arewa mai jagorantan fasahar 5G a Birtaniya

Yusuf Sambo - Hazikin matashin Arewa mai jagorantan fasahar 5G a Birtaniya

A lokacin da manyan masu fada aji a duniya, Amurka da kasar Sin, ke cigaba da sa'insa kan shin wa zai riga kaddamar da fasahar 5G. Wanda ya kai ga shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya kakabawa kayayyakin kasar Sin haraji maras misaltuwa, kasar Birtaniya na kokarin zarra.

Ministar Skotlan dake Birtaniya, Nicola Sturgeon, ta bayyana cewa kasar na kokarin ciran tuta tsakanin kasashen da ke karkashin lemar Birtaniya a fasahar 5G, saboda nan da shekarar 2035, fasar za ta inganta tattalin arzikin kasar da samar da ayyukan yi 160,000.

Dan Najeriya kuma dan Arewa kasar Skotlan ta dogara da shi domin samun wannan fasahar.

Yusuf Sambo - Hazikin matashin Arewa mai jagorantan fasahar 5G a Birtaniya

Yusuf Sambo tare da Ganduje da Bab Ahmad
Source: Facebook

Shin ko kun san Dakta Yusuf Sambo?

Yusuf Abdulrahman Sambo hazikin matashi ne wanda yake jagorantan fasahar 5G a jami'ar Glasgow dake Birtaniya. An haifeshi a shekarar 1988 a jihar Kaduna kuma dan asalin karamar hukumar Ikara ne.

Ya kasance 'da ga Dakta Abdulrahman Sambo, fitaccen likita a Najeriya kuma tsohon mukaddashin sakataren ma'aikatar inshoran kiwon lafiya wato NHIS.

Ya fara karatunsa ne a makarantar Command Children School, Abuja, sannan ya garzaya Zaria Academy dake Shika gabanin zuwa jami'ar Ahmadu Bello inda ya karanci ilimin injiniyancin lantarki.

Ba tare da bata lokaci ba, Yusuf Sambo, ya shilla jami'ar Surrey dake yankin kudu maso gabashin Birtaniya domin digir-gir.

Yusuf Sambo - Hazikin matashin Arewa mai jagorantan fasahar 5G a Birtaniya

Yusuf Sambo lokacin da ya kammala PhD
Source: Facebook

Bayan kammala karatun digir-gir, Yusuf ya dawo Najeriya domin amfanar da al'ummarsa da ilimin da ya samu inda ya karantar na tsawon shekara daya a jami'ar Baze dake birnin tarayya Abuja bayan aikin shara fagge da Suburban Telecoms.

Dubi ga irin hazakarsa da namijin kokarin da yayi a Birtaniya, jami'ar Surrey ta bashi damar karatun doktoransa kyauta kuma ya kammala yana mai shekaru 27 da haihuwa.

A birtaniya, ya kera fasahohi daban-daban musamman a bangaren ilimin 5G.

Yusuf Sambo - Hazikin matashin Arewa mai jagorantan fasahar 5G a Birtaniya

Yusuf Sambo - Hazikin matashin Arewa mai jagorantan fasahar 5G a Birtaniya
Source: Facebook

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel