Enugu: An tabbatar da Ike Ekweremadu a matsayin zababben Sanata

Enugu: An tabbatar da Ike Ekweremadu a matsayin zababben Sanata

Dazu mu ka ji cewa kotun da ke sauraron korafin zaben majalisar tarayya da jihohi a jihar Enugu ta tabbatar da zaben Ike Ekweremadu da aka yi a matsayin Sanata mai wakiltar yankin Enugu.

Kamar yadda rahotanni su ka zo mana daga Jaridar Vanguard da yammacin Litinin, 9 ga Watan Satumba, 2019, an yi watsi da karar da ‘yar takarar APC ta shigar game da nasarar Ike Ekweremadu.

A hukuncin da Alkalai su ka yanke a farkon makon nan, an bayana cewa ‘yar takarar jam’iyyar APC mai harin kujerar Sanatar Enugu ta yamma watau Juliet Ibekaku-Nwagwu ba ta da hujjoji masu karfi.

Sauran Alkalan da su ka zauna a karkashin Mai shari’a Haruna Kereng duk sun yi na’am da wannan hukunci inda aka ce ‘yar takarar APC da ta kai korafi ba ta da kara mai nauyi da zai sa a rusa zaben.

Mai shari’a Haruna Kereng yake cewa Juliet Ibekaku-Nwagwu ta gaza gamsar da kotu kamar yadda ya dace game da ikirarin amfani da ‘yan daba da sabawa ka’idoji da PDP ta yi a zaben da ya gabata.

KU KARANTA: An ba Sanatan PDP gaskiya bayan an fatattaki karar ‘Dan takarar APC

Babban Alkalin da ya yanke hukunci ya bayyana cewa babu gaskiya a da’awar da APC ta ke yi a gaban kotu cewa ‘dan takarar PDP ya yi coge tare da amfani da co ‘yan daba wajen lashe zaben majalisar.

A shari’ar da Kereng ya karanto, ya ce ba a iya nunawa kotu yadda aka yi coge wajen tattara sakamakon ba. Haka zalika shaidu 16 rak mai karar ta iya gabatarwa a cikin kananan hukumomi 5 na shiyyar.

Kotu ta duba korafin da aka kawo a wuraren zabe fiye da 820 da ke cikin Mazabu 91 na kananan hukumomin da ke cikin yankin Enugu ta yamma. Bayan kammala duk bincike an gane cewa PDP ce ta ci zabe.

Tun a 2003 Ike Ekweremadu ya ke wakiltar mutanen Mazabar Enugu ta yamma a majalisar dattawan Najeriya. Sanatan ya shafe shekaru 12 a matsayin mataimakin shugaban majalisa.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng News

Online view pixel