Yanzu-yanzu: Kotun zabe ta fitittiki dan majalisar PDP a Sokoto

Yanzu-yanzu: Kotun zabe ta fitittiki dan majalisar PDP a Sokoto

Kotun zaben yan majalisu ta fititttiki mamba mai wakiltar Sokoto ta Arewa II, Ibrahim Arzika Sarki na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) daga majalisar dokokin jihar.

Alkali Peter Akhimie Akhihiero wanda ya jagoranci zaman ya bada umurnin gudanar sabon zabe a wurare shida na mazabar da hukumar gudanar da zabe ta kasa mai zaman kanta INEC ta soke.

Dan takarar jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a zaben, Hon. Hussaini Tukur Faru, ya kalubalanci alanta Ibrahim Sarki da INEC tayi a matsayin wanda ya lashe zaben ba tare gudanar da zaben cike gurbi kuri'un da ta soke ba.

Alkalin ya bayyana cewa zaben da aka gudanar ranar 9 ga watan Maris, 2019 ba kammalalle bane. Ya ce alanta Arzika Sarki matsayin gwarzon zaben bai dace ba.

Alkali Akhihiero ya umurci hukumar INEC ta kwace takardar nasara daga hannun Arzika Sarki kuma ya biya Hussaini Tukur, N20,000.

A bangare guda, Kotun da ke sauraron kararrakin zaben majalisar dokokin tarayya da ke zama a Abeokuta, babban birnin jihar Ogun, ta soke zaben Kolapo Korede Osunsanya, mai wakiltan mazabar Ijebu ta tsakiya a majalisar wakilai a karkashin jam’iyyar APC.

Kotun zaben ta kuma yi umurnin sake sabo zabe a unguwanni uku cikin kwanaki 90, jaridar Daily Sun ta ruwaito. Mazabar Ijebu ta tsakiya ya hada da kananan hukumomi uku wadanda suka hada da Ijebu Ode, Ijebu North ta gabas da kuma Odogbolu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel