Tattakin mabiya Shi'a daidai yake da ta'addanci - IGP

Tattakin mabiya Shi'a daidai yake da ta'addanci - IGP

Rundunar 'yan sandan Najeriya ta ce tana da masaniyar cewa wasu mambobin kungiyar 'yan uwa Musulmai (IMN), wacce aka fi kira da 'Shia', na shirin gudanar da tattaki domin kawo hargitsi da tayar da tsugune a tsaye a cikin kasa.

A wani jawabi da kakakinta na kasa, DCP Frank Mba, ya fitar ranar Litinin, rundunar 'yan sandan ta ba bayyana cewa, "a kokarinta na dakile duk wasu aiyukan ta'addanci, rundunar 'yan sanda ta samu sahalewar doka a ranar 26 ga watan Yuli wajen haramta kungiyar IMN da dukkan aiyukanta.

"A saboda haka, dukkan wani tattaki ko taron da kungiyar zata yi ya saba wa doka kuma rundunar 'yan sanda zata dauki hakan a matsayin aikin ta'addanci," a cewar jawabin da DCP Mba ya fitar.

DCP Mba ya cigaba da cewa, "a saboda haka, babban sifeton rundunar 'yan sanda na kasa, IGP Mohammed Adamu, ya umarci kwamishinonin johohi da mataimakansa na shiyya da babban birnin tarayya (FCT) da su dauki tsauraran matakai domin hana duk wani tattaki ko tayar da 'tsugune tsaye' da mabiya Shi'a kan iya haifar wa a kowanne bangare na kasa."

Kazalika, IGP Adamu ya bukaci jama'a da su bayar da muhimman bayanai ga rundunar 'yan sanda a kan duk wani shiri da mabiya haramtacciyar kungiyar Shi'a ke yi dangane da tattakin da suke gudanar wa a irin wannan lokaci.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel