Akwai yunkurin kawo hargitsi a Najeriya - DSS

Akwai yunkurin kawo hargitsi a Najeriya - DSS

Hukumar tsaro na sirri (DSS), ta koka kan cewa wasu kungiyoyi da mutane na kulla makirci domin kawo hargitsi a Najeriya da rushe zaman lafiya, tsaro da hadin kan kasar, jaridar Vanguard ta ruwaito.

Koda dai DSS bata ambaci sunayen wadanda ke da hannu da kuma lokacin da ake kulla makircin ba, ta bukaci yan Najeriya da su zuba ido sosai domin kada wadannan makirai su yi masu bazata da mugun nufinsu.

Wani jawabi dauke da sa hannun jami’in hulda da jama’a na hukumar DSS, Dr Peter Afunanya, ya fayyace cewa hukumar na kokarin bin sahun makiran da ke shirya kulla-kullan.

Hukumar ta kuma ba yan Najeriya tabbacin cewa za ta ci gaba da jajircewa akan kudirinta na daidaita kasar kamar yadda ya rataya a wuyanta ya kare kasar daga laifuffuka da duk wani abu da zai zama barazana ga tsaro.

KU KARANTA KUMA: Kotun zabe ta tsige dan majalisa na APC a Ogun, tayi umurnin sake sabon zabe cikin kwanaki 90

A wani labarin kuma mun ji cewa a kokarinsu na kawo karshen aiyukan 'yan bindigar da suka addabi jihohinsu da kisan jama'a ba dare ba rana, gwamnonin jihohin arewa hudu karkashin jagorancin Aminu Bello Masari, sun cimma wata yarjejeniya da takwaransu na jihar Maradi a jamhuriyar Nijar, Alhaji Zakari Umaru.

Jihar Maradi ta jamhuriyar Nijar ta yi iyaka da Najeriya ta jihar Katsina Sokoto, Kebbi da Zamfara.

Tawagar da masari ya jagoranta, ta dira a jamhuriyar Nijar tare da sauran gwamnoni uku; Muhammad Bello Matawalle na jihar Zamfara, Aminu Waziri Tambuwa na jihar Sokoto da Atiku Bagudu na jihar Kebbi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel