EFCC za ta bi kadin Dala biliyan 16 da Obasanjo ya batar kan lantarki

EFCC za ta bi kadin Dala biliyan 16 da Obasanjo ya batar kan lantarki

Rahotanni na zuwa mana cewa EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa za ta fara binciken kudin da ake zargi an sace wajen aikin wutar lantarki a gwamnatin Obasanjo.

Hukumar za ta soma damke wasu da ake zargi da sace tiriliyoyin kudin Najeriya bayan gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nuna cewa za a binciki badakalar da aka tafka a baya.

A dalilin wannan bincike ne jami’an EFCC su ka kama wasu ma’aikatan kamfanin wuta na NDPHC. Obasanjo ya na faman ikirarin cewa bai yi awon gaba da sisin da aka warewa lantarkin ba.

Ana zargin gwamnatin tsohon shugaba Olusegun Obasanjo da batar da biliyan $16 wajen harkar wutan lantarki. Har yanzu ana kuka da cewa babu isasshen wuta a kasar bayan kashe makudan kudi.

KU KARANTA: An bayyana abin da ya hana Jonathan hukunta Buhari a 2011

Hujjar da Obasanjo yake badawa ita ce an kashe wadannan kudi ne wajen ayyukan da hukumar NNIPP ta yi da kuma gina na’urorin samar da wuta ta gas 18 shekaru fiye da goma da su ka wuce.

EFCC ta sha alwashin bankado duk wanda yake da hannu a gwamnatin tarayya wajen batar da kudin wutan. Daga ciki ne ake binciken jami’an NDPHC da laifin wawuran sama da biliyan 80.

Daily Trust ta ce ana tunanin cikin ‘yan kwanakin nan za a sake damke wasu jami’an gwamnati da za a tasa a gaba da ake zargi da hannu cikin badakalar da aka tafla a lokacin PDP ta na mulki.

Daga cikin wadanda za a yi wa tambayoyi cikin ‘yan kwanaki masu zuwa akwai wani tsohon shugaban hukumar TCN wanda aka ba Biliyan 185 domin shigo da wasu manyan na’urorin wuta.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Online view pixel