Har ila yau: Kotu ta soke zaben tsohon gwamna da aka zaba Sanata a APC

Har ila yau: Kotu ta soke zaben tsohon gwamna da aka zaba Sanata a APC

Kotun sauraron korafin zaben mambobin majalisun tarayya da na dokoki dake zaman ta a jihar Abiya ta soke zaben tsohon gwamnan jihar da ya yi mulki a PDP, Orji Uzor Kalu, wanda kuma aka zaba sanata mai wakiltar jihar Abiya ta arewa a karkashin inuwar jam'iyyar APC.

Kotun ta bayar da umarnin sake gudanar da zabe a mazabu takwas dake yankin karamar hukumar Arachukwu da wasu mazabu masu yawa da aka soke sakamakon zabensu a arewacin jihar Abiya a cikin kwanaki 90.

Tsohon gwamna Kalu ya koma jam'iyyar APC ne gabanin zaben shekarar 2015, sannan an bayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben kujerar sanata a cikin wani yana yi mai cike da rudani.

Kalu ya taba yin takarar shugaban kasa a karkashin inuwar jam'iyyar PPA bayan ya kammala zangonsa na biyu a kujerar gwamnan jihar Abiya.

DUBA WANNAN: Majalisar Legas ta yi Alla-wadai da sakin 'yan arewa 123 da aka kama a jihar

Tsohon gwamnan na daga cikin tsofin gwamnoni da har yanzu hukumar yaki da cin hanci da karya tattalin arziki (EFCC) ke tuhuma da tafka badakalar kudi lokacin da suke kan mulki.

Kotun mai alkalai guda uku a karkashin jagorancin jastis Cornelius Akintayo ta yanke hukuncin ne biyo bayan korafin da dan takarar jam'iyyar PDP, Mao Ohuabunwa, ya shigar gabanta a kan bayyana sunan Kalu a matsayin wanda ya yi nasarar lashe zaben kujerar sanatan jihar Abia ta arewa.

A karar da ya shigar a gaban kotun, Ohuabunwa ya zargi baturen hukumar zabe (INEC), Dakta Charles Anumudu, da tafka magudin zabe bayan ya sanar da sakamakon zaben da ya bawa Kalu nasara duk da kasancewar adadin kuri'un da aka soke sun zarce yawan banbancin kuri'un dake tsakaninsa da Kalu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel