Ba lallai sulhu da 'yan bindiga ya yi tasiri ba - Gwamna Zakari Umaru

Ba lallai sulhu da 'yan bindiga ya yi tasiri ba - Gwamna Zakari Umaru

A kokarinsu na kawo karshen aiyukan 'yan bindigar da suka addabi jihohinsu da kisan jama'a ba dare ba rana, gwamnonin jihohin arewa hudu karkashin jagorancin Aminu Bello Masari, sun cimma wata yarjejeniya da takwaransu na jihar Maradi a jamhuriyar Nijar, Alhaji Zakari Umaru.

Jihar Maradi ta jamhuriyar Nijar ta yi iyaka da Najeriya ta jihar Katsina Sokoto, Kebbi da Zamfara.

Tawagar da masari ya jagoranta, ta dira a jamhuriyar Nijar tare da sauran gwamnoni uku; Muhammad Bello Matawalle na jihar Zamfara, Aminu Waziri Tambuwa na jihar Sokoto da Atiku Bagudu na jihar Kebbi.

Da yake gabatar da jawabi yayin rattaba hannu a kan yarjejeniyar, gwamna Zakari Umaru ya ce jami'an tsaro a jihohin hudu sun dade suna aiki tare da takwarorinsu a jamhuriyar domin yakar aiyukan ta'addanci da tabbatar da zaman lafiya a yankin.

DUBA WANNAN: Mayakan kungiyar Boko Haram sun kwace motar yaki, kudi fiye da miliyan N15 a hannun sojoji

"A kan dauki matakai daban-daban domin tabbatar da zaman lafiya. Jihohin Katisna, Sokoto da Zamfara sun zabi yin amfani da sulhu, mu ma a na mu bangaren za mu bi wannan hanyar tare da su saboda aiyukan ta'addanci dake faru wa a can sun iso mana nan," a cewarsa.

Sai dai gwamnan na jihar Maradi ya ce ba kasafai sulhu da 'yan ta'adda ke yin tasiri ba tare da yin kira a yi taka tsan-tsan duk da 'yan bindigar duk da an yi sulhu da su.

"Ana samun wasu tsageru daga cikin 'yan ta'adda dake bijire wa yarjejeniyar zaman lafiya," a cewar gwamna Zakari.

Gwamnan ya kara da cewa alhakinsu ne a matsayinsu na shugabanni su yi maganin tsagerun 'yan ta'addar da kan iya bijire wa yarjejeniyar zaman lafiyar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel