Kotun zabe ta tsige dan majalisa na APC a Ogun, tayi umurnin sake sabon zabe cikin kwanaki 90

Kotun zabe ta tsige dan majalisa na APC a Ogun, tayi umurnin sake sabon zabe cikin kwanaki 90

Kotun da ke sauraron kararrakin zaben majalisar dokokin tarayya da ke zama a Abeokuta, babban birnin jihar Ogun, a ranar Litinin, 9 ga watan Satumba, ta soke zaben Kolapo Korede Osunsanya, mai wakiltan mazabar Ijebu ta tsakiya a majalisar wakilai a karkashin jam’iyyar APC.

Kotun zaben ta kuma yi umurnin sake sabo zabe a unguwanni uku cikin kwanaki 90, jaridar Daily Sun ta ruwaito.

Mazabar Ijebu ta tsakiya ya hada da kananan hukumomi uku wadanda suka hada da Ijebu Ode, Ijebu North ta gabas da kuma Odogbolu.

Kotun zaben karkashin jagorancin Hon Justis Wakkil Alkali Gana, ya soke zabe a wasu unguwanni a fadin kananan hukumomin guda uku.

Dan takarar PDP, Taiwo Shote, ya shigar da kara inda ya kalubalanci kaddamar da Osunsanya a matsayin wanda ya lashe zabe da hukumar INEC tayi a zaben ranar, 23 ga watan Fabrairu.

KU KARANTA KUMA: Kotun zabe ta ba Sanata Clifford Ordia gaskiya a shari'ar jihar Edo

Kotun zaben da take yanke hukunci tayi umurnin cewa tunda tazarar da ke tsakanin wanda ake kara da mai karan mai kai 4,000 sannan yawan adadin kuri’un da aka soke ya kasane 8,800, bai kamata INEC ta kaddamar da Osunsanya a matsayin wanda yayi nasara ba kamar yadda yake a dokar zabe.

Ya ci gaba da cewa kamata yayi hukumar zaben ta kaddamar da zaben a matsayin ba kammalalle ba sannan a sake zabe a unguwanni da rumfunar zaben da abun ya shafa.

Don haka kotun ta soke zaben sannan tayi umurnin sake sabon zabe cikin kwanaki 90.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel