Kwanaki 100 sun yi kadan a gane kokarin Buhari – fadar shugaban kasa

Kwanaki 100 sun yi kadan a gane kokarin Buhari – fadar shugaban kasa

Fadar shugaban kasa ta bayyana cewa kwanaki 100 sun yi kadan a gane kokarin gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari musamman a sabon zangon mulkinsa na biyu, inji rahoton jaridar Guardian.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito kaakakin shugaban kasa Femi Adesina ne ya bayyana haka yayin da yake tattauna da gidan talabijin na Channels, inda yace “Babu yadda za’a yi a fara auna gwamnatin tazarce a cikin kwana 100 saboda gwamnatin ta cigaba daga inda ta tsaya ne.”

KU KARANTA: Gwamnonin Najeriya sun bayyana ma Wike hanyar kashe wutar rusa Masallacin juma’a

Adesina ya cigaba da cewa sabuwar gwamnati kadai ake aunawa da kwanaki 100 na farko, hatta a kasar Amurka da Najeriya ta kwaikwayo tsarin bikin rana 100 na farko ba’a auna gwamnatin tazarce da kwanaki 100, a cewar Adesina.

Amma Adesina ya bayyana cewa gwamnatin Buhari ta cigaba da aiwatar da manufofinta na canji kamar yadda ta fara a wa’adin mulkinta na farko, ya bigi kirji ya kara da cewa idan ma za’a auna gwamnatin Buhari a ma’aunin kwanaki 100, toh sun ciri tuta a bangarorin tattalin arziki, tsaro da kuma manyan ayyuka.

Shugaban kasa Buhari ya lashe zabensa karo na biyu ne bayan ya lallasa babban abokin hamayyarsa, Atiku Abubakar da bambamcin kuri’ miliyan 3 da dubu dari 9 da dari 8 da sittin 9.

A wani labarin kuma, Kotun sauraron korafe korafen zaben gwamnan jahar Kaduna da aka gudanar a watan Maris na shekarar 2019 ta tabbatar da nasarar da Nasir Ahmad El-Rufai ya samu, inda ta bayyana shi a matsayin halastaccen gwamnan jahar.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel