Kotun zabe ta ba Sanata Clifford Ordia gaskiya a shari'ar jihar Edo

Kotun zabe ta ba Sanata Clifford Ordia gaskiya a shari'ar jihar Edo

Mun samu labari daga Jaridar The Nation cewa Alkalan kotun da ke sauraron korafin zaben 2019 a jihar Edo, sun tabbatar da nasarar Sanatan jam’iyyar PDP, Clifford Ordia a zaben da ya gabata.

Kotun da ke karbar karar zaben majalisa a jihar Edo a Garin Benin, ya ba babban Sanatan PDP, Clifford Ordia mai wakiltar Edo ta tsakiya gaskiya a zaben bana a game da karar da APC ta shigar.

‘Dan takarar jam’iyyar APC, John Osagie Inegbedion, ya gaza gamsar da kuliya da kwararan hujjoji cewa PDP ta yi amfani da kudi wajen sayen kuri’un jama’a da kuma murde zaben na 2019.

A hukuncin da kotu ta yi, Alkalai sun bayyana cewa masu tuhumar ba su iya kawo ko da mutum guda da aka saye kuri’arsa da kudi a zaben ba kamar yadda mai shigar da karar ya yi ikirari.

KU KARANTA: Sanatan PDP da ya gamu da hadarin mota bayan dawowa daga wani taro

Kamar yadda mu ka samu labari, Alkalan da su ka saurari karar, sun yi ittifaki cewa hujjojin da Osagie Inegbedion ya gabatar, ba su da wani karfi, inda aka kuma kore wani bidiyon da ya bada.

Kotu ta ce bidiyon da aka nuna na wasu mutane su na dangwala kuri’a bai nuna cewa an tafka magudin zabe. A dalilin gaza gamsar da kotu cewa an yi murdiya, aka yi watsi da wannan kara.

Bayan nan, Alkalan kotun zaben da su ka zauna a cikin Garin Benin, sun yi fatali da wani karar APC da cewa babu dalilin da zai sa matakin da jam’iyya ta dauka, ya yi tasiri a kan ‘dan takararta.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel