Ba ni ne Mahaifin Jaririn da TBoss ta haifa ba Inji Sanata Dino Melaye

Ba ni ne Mahaifin Jaririn da TBoss ta haifa ba Inji Sanata Dino Melaye

Fitaccen Sanatan adawa Najeriya, Dino Melaye, ya karyata jita-jitar da ake yi na cewa shi ne Mahaifin jaririn da tsohuwar Jarumar nan ta shirin Big Brother Naija, TBoss, ta haifa kwanaki.

Sanata Dino Melaye ya nuna cewa sam ba cikinsa ne Tauraruwar nan ta wasan Big Brother Naija da aka fi sani da TBoss ta sauke ba. Melaye ya fito ya karyata wannan ne a shafinsa na zumunta.

Ainihin sunan wannan Taurariya da ta yi tashe shekarun da su ka wuce shi ne Tokunbo Idowu. Kwanaki ne Idowu ta haifi yaro duk da ba ta da miji, kuma ta yi gum game da Mahaifin jaririn.

Daga cikin Samarin da ake zargin ta da su akwai Ubi Franklin, Uti Uwachukwu har da kuma Dino Melaye. Sai dai wannan rabin ‘Yar Najeriya ta karyata cewa akwai wani abu da ya hada ta da su.

KU KARANTA: Gwamnan PDP ya fallasa asirin Gwamnoni na satar kudi a Najeriya

Ga abin da Sanatan ya ke fada a Tuwita:

“A ka’ida kamata ya yi in yi watsi da karyayyakin da ke yawo cewa ni ne Mahafin yaron da Tboss ta haifa. Kowane yaro da aka haifa, Baiwa ce daga Ubangiji ga Mahaifiyarsa.”

Melaye ya cigaba da:

“…Kuma ina taya TBoss murnar samun wannan abin farin ciki. Game da Mahaifin (yaron) kuma, ba ni bane. Ban taba soyayya da TBOSS a Duniya. (Olodo) Dakikai sun ki fahimtar hakan.”

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel