Dan takarar PDP a Kogi yace ya shirya kora Yahaya Bello gida

Dan takarar PDP a Kogi yace ya shirya kora Yahaya Bello gida

Musa Wada, dan takarar jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a zaben gwamnan jihar Kogi da za a gudanar a watan Nuwamba, yayi alkawarin gudanar yakin neman zabensa kan muhimman batutuwa.

A wani jawabi na musamman da yayi, Wada ya mika godiyarsa zuwa ga mutanen jihar Kogi akan goyon baya da suka bashi, a matsayin wanda ya cancanci rike tutar PDP a zaben da za a gudanar nan gaba kadan.

Ya bayyana cewa amanar da aka bashi ya sa ya yanke shawarar yin aiki tukuru da kuma kokari wajen fidda jihar daga rashin iya mulki da cin zarafin martabobin damokardiyya da aka yi tsawo shekaru hudu da suka gabata.

Dan takaran gwamnan har ila yau ya bayyana godiyar shi ga jam'iyyar PDP akan samar da dandamalin “shugabancin mutane a jihar Kogi," inda yake cewa a shirye yake ya kwace mulki daga APC a zaben.

Ya nemi goyon bayan masu biyayya ga jam’iyya, masu karfi, shuwagabanni da dattijai, musamman wadanda suka nemi takaran tikiti da shi, inda yace aikin dake gaba “yana bukatar dukkanmu mu manta da baya mu kuma hada kai don daura gwamnatin PDP wacce zata dauki hidima a hakika a jihar Kogi.”

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Yan shi’a sun sha alwashin yin tattaki duk da haramcin da aka sanya a kansu

Wada yace tun daga lokacin da aka kammala zaben fidda gwani, ya nemi shawarwari daga masu ruwa da tsaki akan manufar gudanar da shugabaci da zaikunshi kowa, tare da ingata rayuwar al'umman jihar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel