Gwamnonin Najeriya sun bayyana ma Wike hanyar kashe wutar rusa Masallacin juma’a

Gwamnonin Najeriya sun bayyana ma Wike hanyar kashe wutar rusa Masallacin juma’a

Kungiyar gwamnonin Najeriya ta shawarci gwamnan jahar Ribas, Nyesom Wike daya baiwa al’ummar Musulman jahar Ribas wani sabon wuri da zasu gina masallacinsu, inji rahoton jaridar Daily Nigerian.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito shugaban kungiyar, kuma gwamnan jahar Ekiti, Kayode Fayemi ya kai ziyarar gani da ido zuwa unguwar Trans Amadi inda aka rusa Masallacin tare da Gwamna Wike, har ma ya bayyana cewa bai ga wani ginannen masallaci da aka rusa ba.

KU KARANTA: Wani hadari mai muni ya yi sanadiyyar mutane 10 a jahar Nassarawa

Fayemi ya bayyana cewa ya kai wannan ziyarar ne sakamakon yamadidin daya biyo bayan zargin rusa masallacin juma’a a Rainbow Town, cikin garin Fatakwal, ya kara da cewa kafin nan sai da yayi magana da gwamnan jahar Ribas ta wayar tarho game da matsalar.

Sai dai Gwamna Fayemi ya shawarci Gwamna Wike kamar haka: “Idan har ba zaka kyalesu su yi gini a wanann fili ba, kuma har sun tafi kotu, amma idan suna son wani wuri na daban domin gina masallacin, ina rokonka ka taimaka ka basu.

“Idan har sun nemi wani sabon wuri don yin gininsu, ban jin hakan ya yi tsauri, za ka iya dubawa ka basu wani wurin domin manufarmu shine inganta kyakkyawar alaka, ba wai kawo rarrabuwar kai ba.” Inji shi.

Da yake nasa jawabin, Gwamna Wike ya bayyan godiyarsa da ziyarar da Gwamna Fayemi ya kai masa tare da kokarin zuwa har inda aka ce akwai masallacin, sa’annan ya bayyana rashin jin dadinsa da yadda wasu suka zuzuta maganar tare da siyasantar da ita.

Amma daga karshe ya bayyana cewa a shirye gwamnatin jahar take ta baiwa Musulmai sabon wuri idan suna da bukatar gina Masallaci.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel