Sanata Nicholas Tofowomo ya na samun sauki a hannun Likitoci – Inji Hadiminsa

Sanata Nicholas Tofowomo ya na samun sauki a hannun Likitoci – Inji Hadiminsa

A Ranar Juma’ar da ta gabata ne Nicholas Tofowomo mai wakiltar Mazabar Ondo ta Kudu a majalisar dattawan Najeriya ya gamu da hadari lokacin da tsautsayi ta rutsa da shi da wasu a mota.

Labari yana zuwa mana cewa a halin yanzu, Sanata Nicholas Tofowomo, ya na samun sauki inda ya ke kwance a gadon asibiti. Wani Hadimin Sanatan ne ya shaidawa Manema labarai wannan kwanaki.

Mista Olumide Akinrinlola wanda ya ke taimakawa Sanatan wajen harkokin yada labarai ya bayyana cewa a halin yanzu Mai gidan na sa ya fara samun sauki a asibiti bayan mummunan abin da ya auku.

Da aka tuntubi Olumide Akinrinlola a waya, ya tabbatar da cewa ‘Dan majalisar ya na murmurewa bayan Likitioci sun duba shi a asibiti. Sanatan ya yi hadarin ne tare da wasu manyan ‘yan siyasan yankin.

KU KARANTA: 'Daliba ta kusa shekawa lahira bayan ta sha maganin kwari a Makaranta

Hakazalila, Hadimin Sanatan na Kudancin Ondo, ya bada labarin yadda hadarin ya auku inda ya ce Ubangidan na sa da wani sun yi karo ne da wata mota a kan hanyarsu ta dawowa daga Ibadan.

A Ranar Lahadi, Akinrinlola ya ce: “Ina so in fadawa jama’a cewa babu dalilin tada hankalinsu, Sanata ya na nan garau, yanzu na yi magana da shi (Ranar Asabar da yamma), ya na samun sauki.

A cewar Mista Akinrinlola, Sanatan ya kusa komawa gida inda ya fadawa ‘yan jarida cewa: “Ina sa ran cewa nan gaba kadan za a sallame shi daga asibiti." Amma bai fadi takamaimen lokaci ba.

Wannan ya zo daidai da abin da wani babban jami’in hukumar FRSC masu kula da hanyoyi watau FRSC ya bayyana bayan ya ziyarci Sanatan a asibiti. Jami’in ya ce Tofowomo ya fara mikewa.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel