Yanzu Yanzu: Yan shi’a sun sha alwashin yin tattaki duk da haramcin da aka sanya a kansu

Yanzu Yanzu: Yan shi’a sun sha alwashin yin tattaki duk da haramcin da aka sanya a kansu

Mambobin haramtacciyar kungiyar nan na Islamic Movement in Nigeria (IMN) wanda aka fi sani da Shi’a, a ranar Litinin, 9 ga watan Satumba, sun sanar da cewar za su yi wani tattaki a gobe Talata, 10 ga watan Satumba.

Kakakin kungiyar IMN, Ibrahim Musa me ya sanar da hakan a wani bidiyo zuwa ga Channels TV a ranar Litinin.

Ya bayyana tattakin a matsayin “tattakin Ashura da suka saba yi duk shekara,” inda ya bayyana cewa hakan zai gudana a fadin manyan birane na kasar.

Ya kara da cewa, za a gudanar da tattakin ne domin juyayin mambobinsu da aka yiwa kisan gilla.

Ya kuma bayyana cewa hakan zai gudana a kasashen duniya da dama domin alhinin mutuwar jikan annabi wanda aka yiwa kisan gilla a ranar 10 ga watan Muharram wanda yayi daidai da gobe Talata, 10 ga watan Satumba.

KU KARANTA KUMA: Masu garkuwa da mutane sun kone gawar wani matashi saboda ba a biya su kudin fansa ba

Kakakin kungiyar ya kara da cewa za a gudanar da tattakin duk da zargin shirin da rundunar yan sandan Najeriya ke yi na tarwatsa taron.

Ya dage cewa lallai mambobin kungiyar Shi’a masoya zaman lafiya ne, kamar yadda addinin Islama ya kasance addinin zaman lafiya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel