Buhari ya bada umarnin kwaso ‘yan Najeriya daga kasar Afirka ta Kudu

Buhari ya bada umarnin kwaso ‘yan Najeriya daga kasar Afirka ta Kudu

Shugaba Muhammadu Buhari ya bai wa Ministan harkokin kasashen wajen Najeriya, Mista Geoffrey Onyeama umarnin daukar matakin gaggawa a kan abinda akeyiwa ‘yan Najeriya a kasar Afirka ta Kudu.

Haka kuma ya bada umarnin a soma kwaso ‘yan Najeriya daga kasar wadanda ke da niyyar dawowa gida ba tare da bata lokaci ba.

KU KARANTA:Yanzu-yanzu: El-Rufa'i ya samu nasara a kotu, anyi yi watsi da karar PDP

Shugaban Buhari ya bada wannan umarnin ne jim kadan bayan da ya tarbi dawowar wata tawaga ta musamman da ya aikawa Shugaba Cyril Ramaphosa na kasar Afirka ta Kudu a makon da ya gabata.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa, Fadar Shugaban kasar Najeriya ta samu wannan bayanin ne daga shugaban hukumar tsaron sirri ta Najeriya wato National Intelligence Agency (NIA), Ahmed Rufai Abubakar.

Cikakken bayani nan tafe……

https://punchng.com/breaking-buhari-orders-evacuation-of-nigerians-from-south-africa/

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Tags:
Online view pixel