Wani hadari mai muni ya yi sanadiyyar mutane 10 a jahar Nassarawa

Wani hadari mai muni ya yi sanadiyyar mutane 10 a jahar Nassarawa

Akalla mutane 10 sun gamu da ajalinsu a sanadiyyar wani mummunan hadari daya auku a karamar hukumar Akwanga ta jahar Nassarawa, kamar yadda rahoton jaridar Daily Trust ta bayyana.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito lamarin ya auku ne a daidai wani mugun hawa da ake yi ma suna ‘Mutuwar yawa’, a tsakanin wata babbar motar Tirela da ta yi dakon Siminti da wasu kananan motoci.

KU KARANTA: Rufe boda ya dakatar da fasa kaurin man fetir daga Najeriya – Inji shugaban NNPC

Jami’an hukumar kare haddura ta kasa, sun hallara a inda hatsarin ya auku domin gudanar da aikin ceto, tare da hadin gwiwar jami’an Sojan kasa da kuma jami’an rundunar Yansanda.

Kwamandan rundunar hukumar kare haddura ta kasa reshen jahar Nassarawa, Ismaila Kugu ya tabbatar da aukuwar lamarin, sa’annan yace zai fitar da cikakken jawabi ga manema labaru bayan sun kammala aikin ceton.

A wani labarin kuma, tsohon ministan shari’a a zamanin mulkin tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, Mohammed Bello Adoke ya bayyana cewa saura kiris ya kashe kansa sakamakon matsin lamba da yake fuskanta daga gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Adoke wanda a yanzu haka ya tsere daga Najeriya ya bayyana haka cikin sabon littafinsa ‘Burden of Service” cewa gwamnatin Buhari ta takura masa bayan ya sauka daga mukamin minista sakamakon faduwa zabe da suka yi a 2015.

Adoke ya lissafa mutane 3 a gwamnatin Buhari da suka sa ya tsani cigaba da rayuwa, daga cikinsu akwai mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo, shugaban EFCC, Ibrahim Magu da kuma Sanata Ali Ndume.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel