Yanzu-yanzu: El-Rufa'i ya samu nasara a kotu, anyi yi watsi da karar PDP

Yanzu-yanzu: El-Rufa'i ya samu nasara a kotu, anyi yi watsi da karar PDP

Kotun zaben gwamnan jihar Kaduna ta tabbatar da gwamna jihar Kaduna, Nasir Ahmad El-Rufa'i, a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar na gaske.

Yayinda ake gabatar da hukuncin, shugaban alkalan shari'ar, Ibrahim Bako, ya bayyana cewa dan takaran jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Isah Ashiru, ya gaza gabatar da hujjoji kan zargin da ya ke yiwa dan takarar All Progressive Congress (APC), Nasir El-Rufai'

A karar da jam'iyyar PDP da dan takarta, Ishan Ashiru, suka shigar, sun bayyana cewa an tafka magudi a zaben gwamnan jihar Kaduna da ya gudana ranar 9 ga Maris, 2019 kuma saboda da haka, kotu ta kwace kujerar gwamnan jihar, Nasir El-Rufa'i.

Amma kotun ta ce jam'iyyar PDP da Isah Ashiru basu kawo kwararrun hujjojin dake nuna cewa lallai an tafka magudi ba saboda haka, jam'iyyar APC da dan takarta, Nasir El-Rufa'i ne suka lashe zaben.

KU KARANTA: Sarkin Saudiyya ya soke dokar biyan Riyal 2000 ga masu aikin Umrah fiye da sau daya a shekaru biyu

A ranar 11 ga watan Maris, 2019, mun kawo muku rahoton cewa hukumar INEC ta alanta gwamna Nasir El-Rufa'i a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Kaduna inda ya doke Isah Ashiru na jam'iyyar PDP.

Ga dai cikakken sakamakon da hukumar zabe na kasa watau INEC ta fitar.

KAURA LG APC – 8, 342 PDP – 38, 764

MAKARFI LG APC – 34, 956 PDP – 22, 301

JABA LG APC – 6, 298 PDP – 22, 976

KUDAN APC – 28, 624 PDP – 22, 022

IKARA LG APC – 41, 969 PDP – 22, 553

KUBAU LG APC – 67, 182 PDP – 17, 074

KAJURU LG APC – 10, 229 PDP – 34, 658

GIWA LG APC – 51, 455 PDP – 19, 834

KAURU APC – 34, 844 PDP – 31, 928

KACHIA LG APC – 30, 812 PDP – 51,780

SOBA LG APC – 55, 046 PDP – 25, 440

ZANGON KATAF LG APC – 13, 448 PDP – 87, 546

SANGA LG APC – 20, 806 PDP – 21, 226

KADUNA TA AREWA APC – 97, 243 PDP – 27, 665

BIRNIN GWARI LG APC – 32, 292 PDP – 16, 901

CHIKUN LG APC – 24, 262 PDP – 86, 261

SABON GARI APC – 57, 655 PDP – 25, 519

LERE LG APC – 71, 056 PDP – 45, 215

JEMA’A LG APC – 21, 265 PDP – 63, 129

KAGARKO LG APC – 21, 982 PDP – 26, 643

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel