Kotun zabe ta tsige wani dan majalisa na PDP, ta kaddamar da dan takarar APC a matsayin wanda ya lashe zaben

Kotun zabe ta tsige wani dan majalisa na PDP, ta kaddamar da dan takarar APC a matsayin wanda ya lashe zaben

Kotun sauraron kararrakin zaben majalisar dokokin tarayya da ke zama a Abakaliki, jihar Eboyi, a ranar Litinin, 9 ga watan Satumba, ta soke nasarar zaben dan majalisa mai wakiltan mazabar Ikwo/Ezza ta kudu a majalisar dokoki tarayya, Lazarus Ogbee.

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kaddamar da Ogbee a matsayin wanda ya lashe zaben da aka gudanar a ranar 23 ga watan Satumba.

Kotu zaben karkashin jagorancin Justis Sika Henry Aprioku ta kuma kaddamar da abokin adawarsa kuma wanda ya shigar da kara, Chinedu Ogar a jam’iyyar All Progressive Congress, (APC) a matsayin wanda ya lashe zaben.

Ogar ya shiga kotu domin kalubalantar sakamakon zaben inda yayi ikirarin cewa hukumar INEC ta rage yawan kuri’unsa domin gain Ogbee yayi nasara.

Kotun ta amince dashi sannan ta dawo da kuri’un da INEC ta soke da farko a wasu yankuna na Ikwo da kuma Onueke da ke Ezza ta Kudu.

KU KARANTA KUMA: Masu garkuwa da mutane sun kone gawar wani matashi saboda ba a biya su kudin fansa ba

Kamata yayi sakamakon zaben ya kasance 36,238 ga APC yayinda na PDP zai kama 33,263.

Kotun zaben takuma umurci INEC da ta yi gagawan ba dan takarar APC takardar shaidar cin zabe sannan ta janye wanda ta ba dan takarar PDP da farko.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel