Masu garkuwa da mutane sun kone gawar wani matashi saboda ba a biya su kudin fansa ba

Masu garkuwa da mutane sun kone gawar wani matashi saboda ba a biya su kudin fansa ba

Wani ma'abocin amfani da dandalin sada zumunta na Tuwita ya wallafa labarin wani matashi da masu garkuwa da mutane suka kashe saboda danginsa sun gaza biyan kudin da aka nema domin fansar shi.

A cewar mutumin da ya yada labarin, masu garkuwa da mutane sun kashe matashin tare da kone gawarsa kurmus, kamar yadda jaridar informationng.com ta wallafa.

Jaridar ta rawaito cewa, masu garkuwa da mutanen sun kira dangin matashin tare da sanar da su inda zasu kwashi tokar gawarsa da suka kone.

"A watannin baya ne masu garkuwa da mutane suka sace abokina, sun kira iyayensa sun sanar da su adadin kudin da suke bukata kafin su sake shi. Daga bisani, bayan basu samu kudin da suka nema ba, sai suka kira iyayensa suka sanar da su inda zasu dauke shi. Amma da iyayen suka je wurin sai gawa suka samu an kone ta 'kurmus', sun kona Jamilu. Iyayensa ma basu iya gane shi ba, kayan jikinsa da takalminsa dake wurin kawai suka iya gane wa."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Mailfire view pixel