Yan sanda sun kama mutanen da suka yi garkuwa da dan majalisa, daliban ABU 3 da wasu a Kaduna

Yan sanda sun kama mutanen da suka yi garkuwa da dan majalisa, daliban ABU 3 da wasu a Kaduna

Yan sanda a Kaduna sun kama gawurtattun masu garkuwa da 25 ciki harda wadanda suka sace Honourable Suleiman Dabo, dan majalisar dokokin jihar Kaduna da wasu dalibai uku dake Jami’ar Ahmadu Bello (ABU).

Kakakin Rundunar yan Sandan, DSP Yakubu Sabo, a wani jawabi da ya gabatar a madadin Kwamishinan yan sanda, Ali Janga a Kaduna, yace masu laifin sun kasance mambobin kungiyar gawurtattun masu Garkuwa da mutane/Yan fashi da makami, wadanda ke daukaka ta’addanci a manyan hanyoyin Kaduna-Abuja da Kaduna-Zaria.

Ya ba da tabbacin cewa ana kokari don ganin an kama sauran mambobin kungiyar tare da makaman aikinsu.

Ya kara da cewa rudunar yan sandan jihar ta karfafa shiri da kuma tsare-tsare akan yanda za’a kai farmaki akan sansanin yan fashin.

KU KARANTA KUMA: Sarkin Musulmi ya yi Allah wadai da Fastoci da Limaman da ke jefa Najeriya cikin rikici

Ya karfafa cewa anyi nasara a samamen da aka kai sannan kuma an raba yan fashin da sansaninsu dake Maigiginya da Gurguzu a karamar hukumar Chukun.

Yayinda ake kokarin tarwatsa yan fashin daga sansaninsu, yace kwamishinan yan sanda ya bukaci mutanenjihar Kaduna da su cigaba da ba yan sanda goyon baya da bayanai masu muhimmanci da zai taimaki rundunar reshen wajen shawo kan matsalolin tsaro na kwanan nan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel