Adoke ya bayyana saura kadan ya kashe kansa saboda matsin lamba daga Osinbajo da Magu

Adoke ya bayyana saura kadan ya kashe kansa saboda matsin lamba daga Osinbajo da Magu

Tsohon ministan shari’a a zamanin mulkin tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, Mohammed Bello Adoke ya bayyana cewa saura kiris ya kashe kansa sakamakon matsin lamba da yake fuskanta daga gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Jaridar Punch ta ruwaito Adoke wanda a yanzu haka ya tsere daga Najeriya ya bayyana cewa gwamnatin Buhari ta takura masa bayan ya sauka daga mukamin minista sakamakon faduwa zabe da suka yi a 2015.

KU KARANTA: Talauci ya jefa wata budurwa cikin mawuyacin hali bayan saurayinta ya kasa biyan sadakin aurenta

Majiyar Legit.ng ta ruwaitoshi yana lissafa mutane 3 a gwamnatin Buhari da suka sa ya tsani cigaba da rayuwa, daga cikinsu akwai mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo, shugaban EFCC, Ibrahim Magu da kuma Sanata Ali Ndume.

Adoke ya bayyana haka ne cikin littafinsa mai suna “Burden of Service”, “A kullum idan na wayi gari naga ana cin mutuncina a shafukan yanar gizo a kan laifin da ban aikata ba sai na ji kamar hukuncin kisa aka yanke min, har na yanke shawarar kashe kaina.’

“Amma daga bisani naga rashin dacewar hakan, saboda idan na kashe kaina za’a ce saboda bani da gaskiya ne, haka kuma za’a cigaba da muzanta iyalaina da aikata abin kunya, don haka naga dacewar na rubuta nawa labarin yadda yake.” Inji shi.

Tsohon ministan ya rasa dalilin da yasa Osinbajo ke neman ganin bayansa, da har zai umarci Magu ya fita farautarsa, kamar yadda yace wani gwamna daga Arewa maso yammacin Najeriya ya tabbatar masa.

“Duk da haka Magu yana da nasa kudurin akaina, saboda wani Sanata ya tambayeshi me yasa yake farautata, sai yace wai ni na mallaki rabin sabon birnin Abuja na Centenary City, sa’annan Sanata Ali Ndume wanda dan garinsu Magu ne shima yana hura min wuta saboda mun kaishi kotu bayan wani dan Boko Haram da aka kama ya fallasa cewa shi ya bashi lambar wayata.” Inji shi.

Bugu da kari Sanatan yace akwai wasu tsofaffin ministocin Jonathan da suka yi aiki tare dake kunno masa wuta a gwamnatin Buhari saboda suna neman alfarma daga gwamnatin, sai su dinga amfani da sunansa da sunan tsohuwar ministar man fetir, Diezani Allison.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit Nigeria

Mailfire view pixel