Da duminsa: Sarkin Saudiyya ya soke dokar biyan Riyal 2000 ga masu aikin Umrah fiye da sau daya a shekaru biyu

Da duminsa: Sarkin Saudiyya ya soke dokar biyan Riyal 2000 ga masu aikin Umrah fiye da sau daya a shekaru biyu

Mai alfarma sarkin Saudiyya, Sarki Salman, ya bayar da umurnin soke dokar biyan karin Riyal 2000 wanda yayi daidai da Naira 193,557 ga masu niyyar aikata aikin Umrah fiye da sau daya cikin shekaru biyu a jere.

Hukumar jin dadin alhazan Najeriya, NAHCON, ta bayyana hakan ne da safiyar Litinin, 9 ga watan Muharram 1441AH, wanda yayi daidai da 9 ga watan Satumba, 2019.

A shekarun baya, hukumomin kasar Saudiya sun kakaba dokar haraji na Riyal 2000 kan duk wanda ya ke son gudanar da aikin Umrah sau biyu ko fiye da haka a kasa da shekaru biyu.

Ga yadda bayanin yake:

Idan mutum yayi aikin Umrah a misali watan Muharram 1439AH, kuma yana bukatan kara zuwa gudanar da wani aikin Umrah kafin Muharram 1441AH, sai ya biya harajin Riyal 2000.

Amma idan ya kwashe shekaru biyu bai bukaci zuwa ba, babu nauyin biyan kudin a kansa. Innama zai biya kudin biza ne tamkar na mai sabon zuwa.

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel